A wannan kakan zabe, cikin sauki mutane suke iya tuna halayya da dabi’un ‘yan siyasa. Haka kuma suna mayar da hankalinsu kan wadanda suka yi silar shiga kuncin rayuwar da ake ciki a yanzu don su mayar masu da biki a akwatun zabe.
Ko da zababbun ‘yan siyasa suna yin haka. Alal misali, El-Rufa’i ya kasa hakuri a lokacin da ya rasa wata dama wanda hakan ya sanya ya rika tsine wa Sanata Danjuma Lah da Sanata Shehu Sani da Sanata Sulaiman Hukunyi. Dalili kuwa shi ne, sun hana shi ciwo wa Jihar Kaduna bashi da zai kasance na farko a tarihi da wata gwamnati a Nijeriya ta taba karbowa na Dala miliyan 350 daga Bankin Duniya.
Ba tare da wata tantama ba, yanzu an gane kokarinsu. Mutane da dama za su tuna cewa wadannan sanatoci sun taka muhimmiyar rawa a zamanin majalisa ta 8 a karkashin jagirancin Bukola Saraki, inda suka ki amincewa da bukatar neman bashin da gwamnatin Jihar Kaduna ta bukata ta duba da bayanin da kwamitin majalisar dattawa kan basussuka na cikin gida da kasashen waje da kuma sanatoci uku daga Jihar Kaduna.
Gwamna El-Rufa’i ya ci gaba da nema da bibiyan bashin duk da sanatoci sun yi watsi da bukatar tasa. A wani taron manema labarai da Gwamna El-Rufa’i ya yi a watan Oktoba shekara ta 2017, ya bayyana cewa wani bangare na kudin za a kashe ne wajen maye gurbin malaman firamare 22,000 da ya kora daga aiki. A watan Nuwambar 2017, a wancan lokacin Suleiman Kwari yana kwamishinan kudi ya bayar da sanarwar cewa kudin za a yi amfani da su ne wajen gine-gine da gyara makarantu da asibitoci da kuma hanyoyi.
Abun mamaki, majalisar dattawa ta 9 karkashin jagirancin Ahmad Lawan sai ta amince da karbo wannan bashin. Sababbin sanatoci biyu Sanata Uba Sani da Sanata Suleiman Hukunyi wadanda suka maye gurbin Shehu Sani da Hukunyi a zauren majalisar sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin an amince da wanna bashin.
Amma kafin a amince da wannan bashin, a watan Fabrairun 2020, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Sani Dattijo ya gaza kare bashi a gaban kwamitin majalisar dattawa kan makasudin karban basussuka na cikin gida da kasashen waje. Wanda a hakan ba a abu ne mai dadi ba.
Kasancewar wannan kudi yana da yawan gaske, mun dan zurfafa bincke a kundayen bayar da bashi na Bankin Duniya da suka sanya a yanar gizonsu. Idanuwarmu sun gano mana wasu abubuwa.
A cewar bayana da suke yanar gizo, bashin an tsara shi ne a watan Yunin 2017, kuma an bayar da Dala miliyan 176 a watan Yunin 2019 kafin majalisar dattawa ta amince a shekarar 2020. Kashi na karshe na kudin an biya a watan Disamba shekarar 2021.
Akwai dokar shekara ta 2007 kan dukkanin basussukan da za a karb sai ya sami amincewar majalisar dattawa. Amma abun mamaki ya aka yi wannan ya tsallake. Bankin Duniya bai iya mayar da martani a kan bukatarmu ba tun a watan Agustan 2022, an kuma fada mana cewa majalisar dattawa ba ta da wani abu a rubuce na cikakken bayanin bashin.
Idan jiha tana bin dokar nan ta FRA da za a su sami bashi mai saukin ruwa kasa da kashi 3.7 cikin 100 da kuma 2.2 cikin 100 yadda abubuwan suka sauka a shekarar 2020 sakamakon annobar Korona. Alal misali bashin IMF da ya bai wa Nijeriya na dala bilyan 3.4 ya karu ne da kashi 1 cikin 100 ne kawai.
A cikin yarjejeniyar bashin Bankin Duniya ya ayyana cewa dole ne a kashe kashi 78 cikin 100 na bashin da aka ciwo wajen ayyukan yau da kullum, a yayin da za a kashe kashi 22 cikin 100 a manyan ayyuka wanda suke zuba jari ne masu sauki kamar gina hanyoyi da sauran gine-gine. Wannan yarjejeniyar ya saba wa dokar FRA 2007. To me sanatoci suke tunani ne har suka amince da wannan bashin?
A batun gaskiya yarjejeniyar yana da harshen damo. Idan bashin an yi amfani da shi a kan yarjejeniyar Bankin Duniya, hakan na nufin an karya dokar FRA ta 2007 kuma aikata hakan babban laifi ne. Idan ba a yi amfani da wannan bashi ta hanyar da ta dace ba, kamar yadda El-Rufa’i da Sanata Kwari da Sanata Uba Sani suka bayyana a lokacin karban bashi, sun aikata babban laifi da za a nemi majalisar kasa ta yi bincike a kai.
Saboda haka ne muka fahimci cewa lallai gwamnati ba ta son a ci gaba da tattauna ko wata magana da ya danganci bashin Dala miliyan 350 na Bankin Duniya da ta ranto, sakamakon abun zai iya sanya wa a tono wani abu kuma.
Bayanai da alamu na nuna cewa an karbi wasu basussukan. Bincike na nun0a cewa ana bin Jihar Kaduna bashi a cikin gida na Naira biliyan 87 da kuma Dala miliyan 587 a waje. Idan ana sauya wannan bashin da farashin dala na Naira 455, ana bin Kaduna bashin Naira biliyan 354, wanda hakan ya sanya ta zama ta fi kowacce jiha ciwo bashi a Nijeriya bayan Lagos.
A wannan matsayi da ake ciki idan aka dubi kikiddigan za a ga cea tattalin arziki yana cikin wani hali. Yanzu za a iya yarda da maganar Buhari da yake cewa talaucin da mutane ke ciki laifin gwamnonin jihohi ne. Su ne suke da alhakkin kula da lafiya da samar da ilimi da ingantaccen ruwan sha da samar da gidaje da sauran abubuwan more rayuwa ga al’umma amma sun gaza yin haka.
A watan Nuwamba an sami karuwar talauci wanda yake nuna cewa Kaduna ce ke kan gaba na matalauta da suka kai miliyan 8 da yaran da ba sa zuwa makaranta, wanda Kano ce ta fi ta da matalauta miliyan 10.5.
Wadannan miliyoyin mutane sun rasa kula da lafiyarsu da ingantaccen abinci da ruwan sha da ilimi da samar da wuraren zama da sauran abubuwan more rayuwa. Rashin aikin yi ya kai kashi 44.3 cikin 100, saboda wannan bashin na Dala miliyan 350 na Bankin Duniya. Rashin tsarin biyan haraji da aka kara wa mutane su rika biya don a sami karin kudaden shiga wanda ake yin sa ba a bisa tsari ba. Ainihin matsala zai fara ne a lokacin da aka fara biyan wannan bashin.
Kamar Buhari, El-Rufa’i na fatan ya da sa wasu mutane su ci gaba kuma su karasa abubuwan da bai kammala ba. An saka wa Uba Sani da takarar kujerar gwamna a karkashin APC, a yayin da Dattijo da Kwari suka tsaya takarar sanatoci.
A lokacin wata muhawara da BBC Hausa ta shirya wa ‘yan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya bai wa magoya bayansa kunya inda ya ka sa yin ingantacciyar magana wanda ake yi da harshensa ta haihuwa. Ko da yake wasu suna tunanin saboda yana kusa da Isa Ashiru ne wanda kwarjininsa ta taba shi.
Abu guda daya da kowa ya kamata ya sani shi ne, gwamnan Kaduna na gaba da zai zo ya kasance wanda zai taimaki kowa.