Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting, ta bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a jiya cewa, ko da yaushe Sin tana adawa da yadda Amurka take siyasantar da tsaron kasa, da sabawa ka’idar kasuwanci, da dokar cinikayyar kasa da kasa, da sanya takunkumi kan kamfanoni masu jarin Sin ba tare da hujja ko dalili ba, wanda hakan na lahanta tsarin samar da kayayyaki, da hada-hadar saye da sayarwar kayayyaki, da ma aikin kirkire-kirkiren fasahohi na duk fadin duniya.
Kaza lika Sin na nacewa matsayin ta na goyon bayan kamfanoninta, da su kare hakki da moriyarsu yadda ya kamata. (Amina Xu)