Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Jihar Enugu kuma dan takarar Sanata a zaben 2023, Sanata Chimaroke Nnamani, da kuma Hon. Chris Ogbu daga jam’iyyar kan zargin yi mata zagon kasa.
Jam’iyyar ta kuma kori mambobinta biyar a Jihar Ekiti, wadanda kuma ‘yan takara ne a babban zabe mai zuwa, wadanda suka hada da; Ajijola Lateef Oladimeji (Ekiti ta Tsakiya); Olayinka James Olalere (Ekiti ta Tsakiya II); Fayose Oluwajomiloju John (Ekiti ta Tsakiya I); Akerele Oluyinka (Ekiti ta Arewa I), da Emiola Adenike Jennifer (Ekiti ta Kudu II).
- Akwai Bukatar Amurka Ta Yi Wa Duniya Gamsasshen Bayani
- Ya Kamata Amurka Ta Dakatar Da Sanyawa Sauran Kasashe Takunkumi Bisa Radin Kanta
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba, wanda ya bayyana korar ‘ya’yan jam’iyyar bakwai a cikin wata sanarwa, ya ce matakin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 10 ga Fabrairu, 2023.
Ya kara da cewa shugabannin jam’iyyar na kasa sun dauki matakin ne bisa shawarar kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar PDP na kasa.
Idan za a tuna cewa jam’iyyar ta dakatar da ‘ya’yan jam’iyyar tara saboda ayyukan da suka saba wa jam’iyyar a ranar 20 ga Janairu, 2023.
Nnamani ya sha kaye a zaben da ya fito neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, a hannun Asiwaju Bola Tinubu.
Idan dai ba a manta ba jam’iyyar ta dage dakatarwar da ta yi wa wasu mambobi biyu a Jihar Ekiti, wato; Funso Ayeni wanda ya tsaya takarar Sanatan Ekiti ta Arewa da Otunba Ajayi Babatunde Samuel, mai neman kujerar tarayya ta Arewa ta biyu a zaben 2023.
PDP ta ce ta dage dakatarwar da aka yi musu ne bayan da suka nemi afuwa kan halinsu, da tabbatar da yin biyayya ga jam’iyyar da kuma sabunta alkawarin da jam’iyyar ta samu a dukkan matakai a zaben 2023 a lokacin da suka bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa.