Gwamnatin jihar Kano ta yi kira da kakkausar murya cewa, ba za ta yi sako-sakon soke lasisin Bankuna da ‘yan kasuwa a jihar da suka ki karbar tsaffin takardun kudade a jihar ba.
Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ne ya yi wannan gargadin a cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai da kula da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar a jihar, inda ya yi nuni da cewa, har yanzu takardun kudaden halatattun kudade ne da ya kamata mutane su dinga amfani da su.
Ganduje ya ce, kotun koli ta zartar da hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin kudin har lokacin da za su bata a hannun jama’a.
A cewarsa, labarai ya riski gwamnatin jihar cewa, ‘yan kasuwa, masu manyan shaguna, bankuna, gidajen sayar da abinci, gidajen sayar da mai da sauransu na kin karbar tsaffin takardun kudaden.
Gwamna Ganduje ya yi nuni da cewa, wasu marasa kishi ne a jihar ke kin karbar tsaffin takardun kudin, inda ya yi nuni da cewa, kin karbar tsoffin kudaden ka iya durkusar da darajar kasuwancin Jihar.
In za a iya tunawa, a makon da ya gabata, gwamnatin jihar ta rufe wasu manyan shaguna a jihar sabida kin karbar tsaffin takardun kudaden.