Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’ar Jihar Inugu da su zaɓi PDP a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi domin su ma su sha romon dimokiraɗiyya daga wajen Gwamnatin Tarayya.
Atiku ya faɗi haka ne a ranar Talata a lokacin taron yaƙin neman zaɓen PDP da aka yi a Inugu.
Ɗan takarar ya ce zaɓen PDP shi zai ƙara kusantar da jihar ga fadar shugaban ƙasa domin a tafi tare da ita.
Ya bayyana jin daɗi kan ɗimbin mutanen da suka fito suka halarci taron, ya ce wannan na nufin da ma can Jihar Inugu jiha ce ta jam’iyyar PDP.
“Ni ne zan zama matakalar da wani ɗan ƙabilar Ibo zai taka ya kai ga zama shugaban ƙasa a nan gaba,” inji shi.
Atiku ya ƙara da cewa: “Ina so ku ci gaba da ba PDP goyon baya domin kuwa gwamnatin da za ta kafa mulkin shugaban ƙasa a nan gaba ta Ibo ce a ƙarƙashin jagorancin Ibo.
“Ina ba ku shawara da ko yaushe ku riƙa tashi ana yin tafiya tare da ku domin ku ma ku sha romon dimokiraɗiyya,” in ji shi.
Sai dai an lura da cewa Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Inugu bai halarci taron ba.
Ugwuanyi, wanda yana daga cikin gwamnonin nan biyar da suka yi tawaye suka ƙi bin Atiku, wato ‘yan gungun G-5, an ce ya tarbi Atiku ne a Gidan Gwamnati a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa kawai.
Dakta Iyorcha Ayu, wanda shi ne Shugaban jami’ar PDP na ƙasa, a nasa jawabin ya bayyana Inugu da cewa jihar PDP ce tun fil’azal.
Ya ce: “Inugu sai PDP; kuma PDP sai Inugu.”
“PDP na cikin jinin ku, kuma na tabbatar da cewa a ranakun zaɓe, wato ranar 25 ga Fabrairu da ranar 11 ga Maris, daga nan za ku zaɓi PDP daga sama har ƙas, kuma daga ƙasa har zuwa sama.”
Bugu da ƙari, ya shawarce su da kada su kuskura su saurari wata jam’iyyar; ya ce: “Rayuwar ku na wajen PDP”.
Kuma ya ce, “Ba sai na tsaya yi maku wani dogon wa’azi ba domin kun riga kun dawo wajen mu.”
Atiku na ci gaba da yaƙin neman zaɓe a sassan ƙasar nan.