Shugabar Matan Jam’iyyar NNPP Reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma shugabar wayar da kan jama’a ta ofishin kamfen na jam’iyyar na kasa Hajiya Saudat Abdullahi, ta kai tallafin kayan abinci gidan gyara hali na Kuje Gami da ‘yanta fursunoni hudu.
Hajiya Saudat a tattaunawarta da manema labaru jim kadan bayan gabatar da kayan abincin ta bayyana cewa, kayan abincin da aka tanada an shirya su ne musamman domin ‘yan uwa da ke cikin gidan gyaran halin.
Ya kamata na tuna da jama’ar da ke cikin gidan duba da cewa suma mutane ne kamar kowa, suna bukatar ci da sha kamar kowa, irin wannan tallafi da nake rabawa ya kamata a ce suma suna samu ba kawai mutanen da suke yawo a waje ba,”in ji ta.
Baya ga tallafin abinci, wakilin LEADERSHIP Hausa idanunsa ya gane masa fursunonin hudu da Hajiya Saudat ta ‘yanta ta hanyar biya musu tarar kudade domin su shaki iskar ‘yanci. Hajiya Saudat tare da tawagarta ta jami’an yada labaru na jam’iyyar ne suka kai ziyarar, inda a karshe ta yi godiya ga hukumar gidan gyaran halin na Kuje bisa damar da ta ba ta domin gabatar da wannan muhimmin aiki.
Mun samu rakiya tun daga shinge na karshe har zuwa inda aka umarce mu ajiye wayoyinmu, kuma mutum biyar ne aka iyakance su shiga ziyara idan kuna da yawa.
Mista Apolabi Julius shi ne jami’in da ya jagorance mu zuwa cikin gida har wurin da ake karbar masu zuwa ziyara domin su gana da wadanda aka ba su izinin ganawa da su, ya gabatar mana da wasu mutum uku da wadanda a lokacin da suka fito cikin mu babu wanda ya yi zaton masu laifi saboda irin shigarsu da kyan suffarsu da kuma yadda suke cikin nutsuwa.
Daya daga cikinsu shi ne sarkin gida, da bai bayyana sunansa ba, daya kuma shi ne Sarkin Musulmi na gida baki daya, wani matashi dan asalin Jihar Adamawa ana kiransa Auwalu Ibrahim Gwamna, wanda ya shafe shekara uku yana jiran hukunci, wato (A Waiting Trail), sai na ukun ana kiransa Mista Doglas, wanda shi kuma ya shafe shekara hudu yana jiran hukunci, sarkin gida kuwa wato ‘President.’
Lokacin da na tambayi Auwalu Gwamna kan yadda ake barin wasu suna zama na tsawon shekara uku zuwa hudu ba tare da hukunci ba, sai ya ce a cikin gidan akwai wadanda suka shafe shekaru 18 zuwa 20 ba tare da hukunci ba.
“Za ka samu mai shekara 18 zuwa 20 har ma a samu wadanda suka haura haka ba tare da an yi musu hukunci ba, kuma wasu ma laifin da suka aikata bai kai a ce an kawo su nan ba, domin wasu ma laifin na su fada ne suka yi ba tare da an yi kisan kai ko jikkatawa ba,” in ji shi.
Da na tambaye shi batun wahalar da suke sha a gidan game da abinci, ya yi bayanin cewa ai a wannan gidan babu matsalar samun abinci da na sha kuma abincinsu mai lafiya ne, in ji Auwalu Ibrahim Gwamna.
Daga nan na tambaye shi yaya suka tsinci kansu a yayin da aka kawo harin da Boko Haram suka kawo? Ya ce wannan lamari ne mara dadin yin bayani.
“Ko da yake abin da ya faru ya faru, a baya kafin a kawo harin adadinmu ya kai misalin kusan 2000, amma bayan kai harin a yanzu ba mu fi mutum 600 a ciki ba. Amma babu abin da ya fi damun duk wani mazaunin wannan gida illa nuna halin ko-in-kula da fannin shari’a ke mana, domin da kutuna suna aiki yadda ya kamata da ba a rika samun cunkuso a gidajen gyaran hali ba, sannan wani babban abin bakin ciki shi ne, tun da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulkin kasar nan bai taba tunanin ya zo ya ga halin da muke ciki ba, amma yau ga wata ita ba ma ‘yar takara bace ta zo har ta bayar da gudunmawar abinci da ‘yanta wasu daga cikinmu,” in ji shi.
Shin wane irin ci gaba wannan gidan ke samarwa ga daurarrun da ke cikin gidan ta fuskar gyaran hali da kuma habaka halayya da tarbiyya? Auwalu Gwamna ya ce, gaskiya a nan dai sai mu yi godiya ga Allah da kuma gwamnati, domin ana gyaran tarbiyya da halayya, ta fuskar koyar da sana’o’i da bayar da ilimi ga kowa.
“Mahaifina babban dan siyasa ne a Jihar Adamawa, nima kuma da dalilin siyasa na shigo gidan nan, amma na zo da kwalina na Digiri, amma yanzu ya kammala digiri na biyu saboda akwai jami’a a ciki da take daukar mutum ta hanyar bayar da tallafin karatu, to idan ka ga mutum bai yi karatu ba to dama can ba shi da niyyar yi,”a cewarsa.
Shin me yake janyo daurarrun da wa’adinsu ya cika aka sallame su daga baya kuma su sake dawowa gidan ta hanyar aikata wasu laifukan? Tambayar kenan da na yi wa Mista Apolabi jami’in da ya jagorance mu zuwa cikin gidan.
Ya ce, wasu daga cikin irin wadannan masu laifi da suke sake aikata laifi a dawo da su gidan sun yi masa bayanin cewa, “A duk lokacin da suka fita daga cikin gidan suka dawo cikin al’umma suna rasa abin da za su yi domin dogaro da kai ko da kuwa a cikin gidan sun koyi wata sana’a saboda rashin wanda zai tallafa musu domin aiwatar da sana’ar, hakan ya kan sa su rasa wani zabi in ba su koma sana’ar da suke yi a da can ba, in ji shi.
Daya daga cikin mutum hudu da aka ‘yanta mai suna Hussaini, wanda ya shafe watanni shida akan tarar 1500, an kama shi ne da laifin yin fad aba kisa ba zubar da jini, ya ce ya yi godiya da wannan tallafi da kuma ‘yanta su da aka yi.
“Tun da na shigo gidan nan ko da labari ban taba ji an ce wani dan siyasa ya zo ziyara ba duk da kuwa ana ta shirye-shiryen zabe sai wannan baiwar Allah, muna godiya sosai,” in ji shi.
Gidan gyaran hali na Kuje gida ne da ya tare manya da kananan masu aikata laifi da suka hada da ‘yan fashi da makami da sauransu. Sai dai shi wannan gidan gyaran hali ya bambanta da sauran gidajen gyaran hali ta fanni daban-daban musamman bangaren tsaro, tsaron kuma ta fuska biyu.
Fuska ta farko ainihin inda aka gina shi, wuri ne da idan ba wanda yake rayuwa a yankin ba wurin yana da ban tsoro, hakan na nuni da idan har ba shirya wa aka yi ko kuma izin mutum ya je wurin ba yana wahalar a shiga wurin kai tsaye.
Akwai shigaye akalla guda biyar na jami’an tsaro nau’i daba-daban wadanda duk wand aka samu sai ya bincike abin da ka zo da shi.
Fannin tsaro na biyu kuma, akwai wadatattun jami’an tsaro da suka hada da sojoji ‘yan sanda Cibil Deffence da kuma jami’an tsaro na musamman wato ‘Special Force’ wadannan duk suna makamai gami da sanya ido kan motsin duk mai zuwa.
A karshe mun ga yadda jama’a ke ziyartar ‘yan uwansu cikin tausayi da alhini musamman idan lokacin rabuwa ya yi. Babban abin da ya bani tausayi shi ne, lokacin da muka kammala ziyararmu sai na ga duk sun koma cikin gi mu kuma mun fito mun tafi gidajenmu.
Daga cikin wadanda suka raka ta akwai lauyanta Barista Idris SAN, Alhaji Nasiru Isa Garun Malam, Sanusi Kwankwasiyya da sakatariyarta Zulai.