Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kar ya sake a karkashin mulkinsa ya bari wata kungiya, musamman kungiyar neman kafa kasar Biafara (IPOB) ta hana ‘yan Nijeriya yin zabe.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya fitar a ranar Talata, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda IPOB ke barazana ga zaben 2023 a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.
- Za A Kira Taruka Biyu A Farkon Wata Mai Zuwa
- Arewa An Sha Mu Mun Warke, Bai Kamata Mu Koma Gidan Jiya Ba – Matasan Arewa A Kudu
Kungiyar ta koka da yadda shuwagabanni, dattijai da ‘yan siyasa daga yankin da sauran sassan Nijeriya suka yi gum da bakunansu kan wannan barazana mai hatsari, wanda ta ce yana da matukar tayar da hankali.
Kungiyar ta jaddada cewa ‘yan NIjeriya na son a gudanar da sahihin zabe da kuma mika mulki cikin lumana zuwa gwamnati mai zuwa, inda ta ce babu wata kungiya da za a bari ta jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali ta hanyar barazana ga zabe da zaman lafiya a kasar nan.
Ta ce: “Wadannan barazanar na biyo bayan hare-haren da ake kai wa gine-ginen gwamnati da kashe-kashe, ciki har da kashe ‘yansanda a yankin. Idan har ba a dauki matakan da suka dace ba, wadanda ke gudanar da ayyukan rashin bin doka suna iya dauka cewa za su yi nasara.
“Duk wani yunkuri na yin katsalandan a ‘yancin ‘yan Nijeriya na shiga hurumin hana su zaben shugabanninsu, babban hari ne ga diyaucin Nijeriya kuma matakin da ya kamata a bijire masa ne.”
A cewar kungiyar, barazana ga zabuka babbar barazana ce ga tsarin dimokuradiyya da kuma ginshikin da al’ummar kasar suka dogara a kai, inda ta kara da cewa, idan har ta samu nasara, barazanar za ta nuna cewa za a fara wasu rikice-rikicen da kasar za ta kasa farfadowa.
“Kungiyar tana kira ga gwamnatin Shugaba Buhari da ta tabbatar da halaccin ikonta a kan duk wata kungiyar da ba ta da doka a kowane sashe na kasar nan tare da tabbatar da cewa ba a hana masu kada kuri’a ko barazana ba.”
Haka kuma, ta lura cewa dole ne shugabanni su fito fili su yi Allah wadai da wannan munanan barazanar tare da tabbatar wa ‘yan kasa masu kada kuri’a cewa za su iya yin hakan. Ta bayyana cewa dole ne ‘yan siyasa masu son shugabanci su fito su yi Allah wadai da wannan barazanar.
Ta ce don kauce wa shakku, barazanar da kungiyar da ke yankin kudu maso gabas ke yi na tsorata masu zabe, inda ta jaddada cewa wadanda ke bayansu su sani cewa za a yi musu tirjiya.
Kungiyar ta yi nuni da cewa so da yawa tana nanata matsayarta da kuma sauran kungiyoyin da ke kishin kasa masu muradin ganin an gudanar da zaben 2023 a duk fadin Nijeriya.