A yau ne, kasar Sin ta fitar da wani sabon bangare na bayanai daga tarin bayanan da aka sanya a kan na’urar bincike ta Chang’e-4 a shafin intanet na tsarin fitar da bayanan duniyar wata da taurari.
Rukunin bayanan sun hada da megabites 3,991.1 na fayilolin bayanai guda 803 da aka samu ta hanyar tsari na kimiyya guda hudu a kan kumbon saukar Chang’e-4 tsakanin ranar 26 ga watan Disamban shekarar 2021 da kuma ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2022.
A ranar 3 ga watan Janairun shekarar 2019 ne, kumbon Chang’e-4, wanda aka harba shi a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2018, ya sauka cikin nasara a karo na farko a cikin koramar Von Karman dake cikin tafkin kudancin Pole-Aitken a bangaren wata mai nisa. Ya zuwa yanzu, na’urar Yutu-2 ta yi tafiyar kimanin mita 1,500 a gefen wata mai nisa.(Ibrahim)