Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC) ya ce yana da lita biliyan 1.8 na man fetur a kasa da zai wadata kasar nan.
Mai magana da yawunta, Malam Garbadeen Muhammad, ya bayyana haka a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce yawan man fetur din da aka samu zai dauki tsawon kwanaki 30.
- Kasashe Masu Tasowa Sun Zargi Kasashen Yamma Da Nuna Jahilci
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Kan Zargin Mallakar Kudaden Jabu A Jihar Kebbi
Ya yi bayanin cewa lita miliyan 805.35 na man na cikin rumbunan ajiya a fadin kasar nan, yayin da har yanzu lita biliyan daya na cikin tasoshin mai.
Ya kara da cewa a kokarin da ake na tabbatar da samar da man fetur, NNPC na yin duk mai yiwuwa don kawo karshen karancin man da ake fama da shi.
“Kuma ana sa ran za a kara samar da man fetur lita miliyan 884 nan da ranar 28 ga watan Fabrairu.
“A watan Maris, 2023, ana sa ran jimillar lita biliyan 2.3 na man fetur, yayin da kimanin lita biliyan 2.8 cikin kwanaki 42, ,” in ji Muhammad.