Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Isah Idris Jere, ya bayyana tsarin amfani da tantance bayanan shige da fice (MIDAS) a matsayin wani tsari da ya inganta iyakokin Nijeriya da sauya fasalin yadda ake ta’asa a iyakokin kasar nan.
Jere, ga shaida haka ne wajen kaddamar da sabuwr cibiyar horaswa ta musamman ‘Training and Reference Centre’ a ranar Alhamis.
- INEC Ta Fara Raba Kayan Aikin Zabe A Adamawa
- Kungiyoyi Magoya Bayan Buhari-Osinbajo Sun Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Zabi Atiku Na Jam’iyyar PDP
Ya kara da cewa, “Shirin MIDAS, ta hanyar amfani da shirin EABDS II tare da tallafin gwamnatin kasar Denmark ya kai ga asassa shirin a manyan wuraren sanya ido a filayen jirgin kasa da kasa guda biyar a Nijeriya ciki har da wannan cibiyar horon.”
Shugaban, ya ce duk da kalubalen da harkar shige da fice ke da fuskanta a a fadin duniya musamman a iyakoki, hukumarsa bisa goyon baya da taimakon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu nasarar fito da tsare-tsare da shirye-shiryen da suka taimaka sosai wajen dakile da shawo kan matsalolin da ake fama da su a kan iyakoki da harkar safara ba bisa ka’ida ba.
Shugaban na NIS, ya jinjina tare da yaba wa gwamnatin kasar Canada da Denmark kan tallafinsu wajen sabunta cibiyar horon inda ta ingata adadinta daga 15 zuwa 40 da suka kunshi cibiyar koyo ta Intanet, babban dakin horo, dakin adana bayanai, sashen kula da MIDAS da sauransu.
Ya ce, wannan taimakon tabbas zai taimaka wa hukumar wajen kara samun nasarori wajen kyautata tsaron iyakoki da shawo kan lamuran da suka shafi shige da fice.
Ya kuma kara da cewa an kuma sake samun wasu tallafin na’urorin sanya ido da suka hada da VSC da aka sanya a cibiyoyin aikin hukumar a filayen jirgi guda biyar wadanda suka taimaka sosai wajen saukin gane bayanan matafiya da taimaka wa wajen zurfafa bincike cikin sauki domin kyautata tsaron iyakokin kasar nan.
Kwanturolan ya kara da cewa, tabbas samar da cibiyar horaswar za ta taimaka musu wajen bai wa jami’ansu horon da ya dace da zai kara musu kwazo wajen gudanar da aikinsu.
Da yake jinjina kan tallafin da suka samu daga IOM da kasashen da suka taimaka, ya nanata aniyar Gwamnatin Tarayya a karkashin sanya idonsa wajen kara himma da kwazo wajen kyautata tsaron iyakokin Nijeriya zuwa ga aikin matakin aiki na kasa da kasa.