Shugaban kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya ce yakin da ake yi a Ukraine na iya daukar shekaru da dama kafin a kawo karshensa.
Yayin tsokaci kan halin da ake ciki, Stoltenberg, ya ce samar da makamai na zamani ga sojojin Ukraine zai taka muhimmiyar rawa wajen ‘yantar da yankin Donbas na gabashin kasar daga hannun Rasha daga hana ragowar biranen yankin shiga hannunta.
- Mai Juna Biyu, Mai Yi Wa Kasa Hidima Da Wasu Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Bayelsa
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Hadari Da Tsawa Na Kwanaki 3 Daga Ranar Litinin
Gargadin NATO na zuwa ne yayin da Rasha ta kara kaimi wajen kai hare-hare da zummar kwace iko da gabashin kasar Ukraine, ita kuwa kungiyar Tarayyar Turai ta amince da bai wa Ukraine din damar zama ‘yar takarar shiga cikinta.
Shi ma dai, Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, wanda ya ziyarci Kyiv a ranar Juma’a, ya ja hankalin da cewar ga dukkanin alamu yakin na Rasha da Ukraine zai dauki tsawon lokaci, inda ya bukaci kara yawan taimakon makaman da ake bai wa Ukraine.