Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad, ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa da ke gudana a halin yanzu tare da nuna kwarin guiwarsa na cewa dan takarar PDP zai iya samun gagarumar nasara.
Bala wanda ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta Bakin Dutse mai lamba OO8 da ke yankin Dan Kungibar a Yalwan Alkaleri, ya jinjina bisa yadda na’urar tantance masu zabe BVAS ke aiki na tare da wani matsala ba.
- Motsa Jiki Na Hana Kamuwa Da Muggan Cututtuka -WHO
- Da Dumi-Dumi: Har Yanzu Jami’an INEC Ba Su Isa Rumfar Zaben Tinubu A Legas Ba
Bala wanda ya kada kuri’ar tare da rakiyar matarsa, Aisha Bala wajajen karfe 10:30am ya yi fatan za a kammala zaben cikin kushin lafiya.