Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya jefa kuri’arsa a Tambuwal, inda ya ce jam’iyyarsa ta PDP za ta kai ga nasara.
Tambuwal wanda ke takarar Sanata a Sakkwato ta Kudu, ya jefa kuri’a a rumfa mai lamba 033 da ke Sakandaren Al’umma ta Tambuwal, ya bayyana cewar jam’iyyar PDP na tsammanin gagarumar nasara.
- Manoman Alkama 50,000 Suka Samu Tallafi A Jihohi 13 —FMAN
- Zaben 2023: ICPC Ta Damke Wani Mutum Da Tsofaffin Kudi Na Miliyan 2 A Bauchi
Gwamnan wanda ya halarci wajen zaben bayan 12 na rana, ya bayyana matsalolin rashin fara zaben a kan lokaci da rashin kai kayan zaben lokacin da aka tsara, da rashin fahimtar na’urar zaben.
Ya ce duk da ‘yan matsaloli nan da can zaben na gudana lafiya musamman a cewarsa kasancewar an shaidi al’ummar Sakkwato da son zama lafiya.
Wakilinmu ya labarto cewar an samu fitowar dimbin jama’a a zaben.
Hakan nan mata sun fi maza yawa, haka ma an samu fitowar mutane masu fama da lalura ta musamman.