Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya doke babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a jih6ar Zamfara.
Nasarar Tinubu ta fito fili bayan sakamakon zaben kananan hukumomi 14 na jihar da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana a Gusau, babban birnin jihar.
- Tawagar Masu Aikin Jinya Ta Kasar Sin Dake Kasar Togo Ta Yi Aikin Jinya Kyauta
- Atiku Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Jihar Kebbi
Mista Tinubu ya yi nasara a kananan hukumomi 12 yayin da Atiku ya yi nasara a guda biyu.
A sakamakon da hukumar zaben ta bayyana a matakin jiha, Tinubu ya samu kuri’u 298,396 yayin da Atiku ya samu kuri’u 193,978.
Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya samu kuri’u 4,044 yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 1,660.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp