• English
  • Business News
Monday, September 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Laifi Tudu, Ka Hau Naka Ka Hango Na Wani

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Laifi Tudu, Ka Hau Naka Ka Hango Na Wani
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kasar Sin ta bayyana adawarta da matakin Amurka na kakabawa wasu kamfanoninta takunkumi bisa dalilai masu nasaba da rikicin Rasha da Ukraine.

Hausawa kan ce, laifi tudu ne ka hau naka ka hangi na wani. Abu ne da kowa ya sani cewa, Amurka ita ce ta ingiza Ukraine shiga halin da take ciki yanzu haka, haka kuma, ita da kawayenta ne ke ci gaba da ruru wutar wannan rikici da ya shafe shekara guda ana yi.

Amma sai ta gaza ganin laifinta na zuba makudan kudi har sama da dala biliyan 46 wajen samar da makamai ga kasar Ukraine, wadanda za a yi amfani da su wajen haifar da asara da illa, maimakon karkatar da su ga abubuwan da al’umma za su amfana, inda take neman shafawa kasar Sin bakin fenti. Kasar Sin din da ta tsaya tsayin daka wajen kaucewa daukar bangare a rikicin, inda ta nace cewa, hanya mafi dacewa ita ce tsagaita bude wuta da hawa teburin sulhu.

Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kamfanonin Sin takunkumi, matakin dake nuna yadda kasar ke nuna isa da danniya da kokarin babakere a duniya, domin kakaba takunkuman ba huruminta ba ne, kana bai samu goyon baya ko sahalewar kwamitin sulhu na MDD ba, kuma baya bisa doron dokokin kasa da kasa.

Shin Amurka ta dauki wannan mataki ne saboda rikicin Ukraine ko kuma saboda wani boyayyen muradi na ta? Shin me ye laifin Sin na kin goyon bayan wani bangare da nacewa ga neman sulhu? Za a iya cewa, Amurka na da wata manufa ta daban kamar kullum, kamar yadda ta saba neman duk wata kafa ko dalili na kuntatawa kamfanonin Sin da zummar dakile ci gaban kasar da bata mata suna a duniya.

Labarai Masu Nasaba

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata

Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa

Kasar Sin ta sha nanata cewa, bata da burin danniya ko babakere. Haka kuma kofarta a bude yake na bayyana dabarunta ga kasashe masu son koyi da ita don samun irin nata ci gaba. Don haka, kamata ya yi Amurka ta ajiye makaman yakinta kan kasar Sin, ta koyi dabarun neman ci gaban tattalin arziki da raya al’ummominta ta hanya mafi dacewa a sabon zamani, maimakon nacewa wajen bata suna da shafa bakin fenti da kuntatawa kamfanonin kasar Sin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Aringizon Kuriu Ya Sanya Hukumar Zabe Ta Soke Zaben Sanatan Zamfara Ta Tsakiya Da Na Majailisar Wakilai

Next Post

Gogaggen Dan Jarida, Shehu Saulawa Ya Kwanta Dama

Related

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata
Daga Birnin Sin

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata

48 minutes ago
Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa

3 hours ago
Xi Jinping Ya Gana Da Narendra Modi 
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Narendra Modi 

21 hours ago
Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO

22 hours ago
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Farfado Da Kasa Bisa Karfin Ruhin Turjiya Ga Zalunci
Daga Birnin Sin

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Farfado Da Kasa Bisa Karfin Ruhin Turjiya Ga Zalunci

23 hours ago
Kasar Sin Ta Inganta Wuraren Tunawa Da Tarihi Don Bikin Samun Nasara Kan Zaluncin Japanawa
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Inganta Wuraren Tunawa Da Tarihi Don Bikin Samun Nasara Kan Zaluncin Japanawa

1 day ago
Next Post
Gogaggen Dan Jarida, Shehu Saulawa Ya Kwanta Dama

Gogaggen Dan Jarida, Shehu Saulawa Ya Kwanta Dama

LABARAI MASU NASABA

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata

Antonio Guterres: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Sanin Ya Kamata

September 1, 2025
Tinubu Ya Yi Adalci Ga Dukkan Yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Tinubu Ya Yi Adalci Ga Dukkan Yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

September 1, 2025
Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Kasar Pakistan: Xi Jinping Shugaban Kasa Ne Mai Hangen Nesa

September 1, 2025
Ina Da Yaƙinin Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen 2027 — Wike

Ina Da Yaƙinin Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen 2027 — Wike

September 1, 2025
Gwamnan Neja Ya Kori Kwamishinoninsa Gaba ÆŠaya

Gwamnan Neja Ya Kori Kwamishinoninsa Gaba ÆŠaya

September 1, 2025
Ƴansanda Sun Gano Motocin Sata 2 A Adamawa

Ƴansanda Sun Gano Motocin Sata 2 A Adamawa

September 1, 2025
Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan

Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan

September 1, 2025
Isak Na Dab Da Zama ÆŠan Wasa Mafi Tsada A Tarihin Firimiya

Isak Na Dab Da Zama ÆŠan Wasa Mafi Tsada A Tarihin Firimiya

September 1, 2025
Rashin Amincewa Da Tsarin Ƴan Kudancin Kaduna Ya Sa Suka Yi Min Mummunar Fassara – El-Rufai

Rashin Amincewa Da Tsarin Ƴan Kudancin Kaduna Ya Sa Suka Yi Min Mummunar Fassara – El-Rufai

September 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Na Shiri Da Ƴan Bindiga, Tana Ba Su Biliyoyi — El-Rufai

Gwamnatin Tarayya Na Shiri Da Ƴan Bindiga, Tana Ba Su Biliyoyi — El-Rufai

September 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.