Kungiyoyin fararen hula (CSOs) sun bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta yi watsi da kin amincewa da ‘yan takarar da aka mika mata sunayensu ba tare da sun shiga zabukan fitar da gwanaye da aka gudanar a jam’iyyunsu ba.
CSOs din sun kuma jawo jawo hankalin jam’iyyun siyasa da cewa su tabbatar da sun maida sunayen asalin wadanda suka shiga zabukan fitar da gwanaye a maimakon maye sunayensu da wasu da ba su ma shiga zabukan ba.
LEADERSHIP ta labarto cewa, jam’iyyar APC ta gabatar da jerin sunayen wasu ‘yan takarar da ba su ma shiga aka dama da su a zabukan fitar da gwanaye na jam’iyyar ba.
Kungiyoyin da suka zanta da LEADERSHIP kan wannan batun su ne: Transition Monitoring Group (TMG) Transparency International (TI) da kuma Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC).
Shugaban COS, Awwal Musa Rafsanjani, ya misalta Mika sunayen wadanda ba su shiga zabukan ba a matsayin rashin adalci mafi girma, ya kuma kara da cewa hakan take demokradiyya ne kai tsaye.
“Ta yaya mutumin da bai fita takarar fitar da gwani ba zai kasance dan takarar jam’iyyar a zaben 2023?” Rafsanjani ya tambaya.
“Mutane su na yin hakan ne don rigar mulki da suke da shi, ya kamata INEC ta yi watsi da irin wannan ta tsaya kan gaskiya
“Mutane su shiga takarar zabukan cikin gida. Kawai sai INEC ta zo ta amshi sunan wanda bai shiga takarar ba duk kuwa da cewa Jami’anta sun bi sawun zabukan, wannan karan tsaye wa doka ne,” a cewar CSOs din.
Kes Din Lawan, Akpabio Kai Tsaye Ya Take Dokar Zabe, Cewar SANS
Manyan lauyoyi a Nijeriya sun yi suka kan canza sunayen wasu da suka ci zabukan fitar da gwanaye da wasu da ba su shiga zabukan cikin gida ba, su na masu misalta hakan a matsayin rashin mutunta doka da oda.
Kayode Enitan (SAN) ya shaida cewar akwai bukatar INEC ta ki karban sunan duk wanda bai sjiya zabukan fitar da gwani ba lura da sashin dokar zabe ta 31 da 33.
Ya ce, “A fayyace yake bisa doron doka na canza ‘yan takara bayan zaben fitar da gwani, sashin dokar zabe na 31 da 33 ya bayyana a zahirance cewa ana canza dan takara ne kawai idan wanda ya ci ya janye bisa radin kashin kansa ko ya mutu.”
Ya kara da cewa, “Idan ‘yan takara sun janye bisa kashin kansu ko sun mutu, sabon zaben fitar da gwani jam’iyyar za ta gudanar.
“INEC ba za ta karbi sunan wani da aka canza da bai fito ta hanyar gudanar da sabon zaben fitar da gwani ba bayan mutuwa ko janyewar wanda ya ci da fari.
Machina Ya Ce Zai Dauki Matakin Shari’a Kan Tikitinsa Na Sanatan Yobe Ta Arewa
Kazalika, wanda ya ci zaben fitar da gwani na Sanatan Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Hon Bashir Sheriff Machina, ya bayyana cewar, ya tabbatar jam’iyyar ta mika sunan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ga INEC a maimakon nashi sunan.
Machina, wanda ya yi magana ta bakin Kakainsa, Hussaini Mohammed Isa, ya ce za su dauki matakin shari’a domin tabbatar da adalci, ya ce ba zai lamunci abun da aka masa ba.