Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairu, kuma jam’iyyarsa za ta tabbatar wa duniya cewa ta yi nasara.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja.
Dan takarar jam’iyyar LP, wanda ya bayyana a bainar jama’a na farko tun bayan zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya ce zaben ya gaza cimma mafi karancin ma’auni na gudanar da zabe mai inganci, don haka zai tunkari kotu domin kwato kujerarsa.
Obi ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar LP da magoya bayansa a kasar nan da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga watan Maris mai zuwa a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp