Shugaba Muhammadu Buhari na wata ziyara ta kwana daya a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Buhari ya isa Maiduguri ne da misalin karfe 11 na safe, inda yake tare da rakiyar manyan jami’an gwamnatin tarayya.
- Peter Obi Da Jam’iyyarsa Ta Labour Sun Ce Su Ne Suka Yi Nasara A Zaben Shugaban Kasa Ba Tunibu Ba
- PDP Da Jam’iyyun Adawa Na Shirin Hade Kai Su Kayar Da APC A Zaben Gwamnan Kwara
Shugaban ya samu tarba daga gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum da sauran tawagar gwamnatinsa.
Ana sa ran zai gana da ‘yan kasuwar da suka rasa shagunansu a wata gobara a babbar kasuwar jihar da kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki.
A ranar Lahadi ne dai aka waye gari babbar kasuwar Monday Market da ke Maiduguri ta kone kurmus sakamakon tashin wuta.