Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Kodibwa Alassane Ouattara, sun aikewa juna sako a yau Alhamis, don taya murnar cikar shekaru 40 ta kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen 2.
Cikin sakonsa, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, kasashen Sin da Kodibwa sun yi ta kokarin nunawa juna sahihanci da kauna, da marawa juna baya kan batutuwan da suka shafi moriyarsu, cikin shekaru 40 da suka gabata. Kasar Sin na son kara kyautata huldar dake tsakaninta da Kodibwa, don samar da dimbin alfanu ga al’ummun bangarorin 2.
A nasa bangare, shugaba Ouattara na kasar Kodibwa ya ce, kasarsa na godiya ga kasar Sin kan yadda take kokarin ba da taimako a fannonin gina kayayyakin more rayuwa da raya bangaren makamashi a kasar Kodibwa. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp