Wani jami’in dan sanda ya kashe buduwarsa ta hanyar harbe ta, inda ta mutu har lahira daga bisani kuma ya bindige kansa shi ma ya mutu har lahira.
Lamarin wanda ya da misalin karfe 8 na safiyar Alhamis, marigayin ya harbe ta ne harabar wata makaranta da ke a garin Ilorin a Jihar Kwara.
- Zabe Gwamna: PDP Ta Nemi Hadakar Wasu Jam’iyyu Domin Kayar Da APC A Kaduna
- Kamfanin Ericsson: Kamfanonin Sadarwa Na Kasar Sin Sun Gaggauta Rungumar Fasahar 5G
Dan sanda wanda MOPOL ne, an bayyana sunansa da Olalere Michael kuma yana aiki ne a Ilorin.
An ruwaito cewa, ya kuma yi aiki a gidan gwamnatin jihar.
Wasu mazauna a yankin sun ce, dan sandan ya biyo budurwar tasa ne har makarantar a cikin motarsa kirar Toyota Corolla bayan da ta zo sauke ‘yarta, kafin ya yi amfani da bindigar sa kirar AK-47 ya harbe ta a kirjinta har sau uku, inda ta mutu a nan take ya kuma harbe kansa.
Wasu mazauna a yankin sun ce, kafin wannan aika-aikar a kwanan baya, ya ziyarci gidansu Tosin da ke kan titin Erin Ile a yankin Gaa Akanbi, inda ya kai mata hari kan wata takardama da ba su riga sun warware ba.
Kakkin rundunar ‘yansandan jihar, Okasanmi Ajayi ya danganta lamarin da harka ce ta soyayya a tsakanin mamatan biyu, inda ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike.