A kwanan nan, yayin da ya yi hira da babban gidan rediyon da talabijin na kasar Sin wato CMG, shugaban kasar Belarus Alexander Grigoryevich Lukashenko ya yi nuni da cewa, Amurka da kasashen yamma suna kawo tarnaki ga tattaunawar lumana, don haka ya kamata Rasha da Ukraine su daina ākashe-kashe tsakanin āyan uwaā.
Lukashenko ya bayyana cewa, āDa farko dai, Rasha ta ba da shawarar gudanar da tattaunawa, mun shiga tare da gudanar da wannan aiki, amma daga baya mun ga cewa, sun zabi kin tattaunawar lumana, shi ya sa ya kamata a yi amfani da damar da ta dace don daina kashe-kashe dake tsakanin āyan uwa, a kuma daina rikicin. Duk da haka, karshen ko wane yaki shi ne zaman lafiya, kuma za a kawo wannan karshen yakin ne ta hanyar zaman lafiya. Abu mai muhimmanci shi ne, mutane nawa ne za su sadaukar da kansu, kuma don me za su saudaukar da kansu. Hanyar da za a bi kawai ita ce zaman lafiya.ā
Yayin da aka ambaci batun sojojin Amurka da suka harbo balan-balan maras matuki na Sin, Lukashenko ya nuni da cewa, wannan wani wasan kwaikwayo kawai ne, mummunan aiki ne. Bai kamata Amurka da Amurkawa su yi wannan abin ba.(Safiyah Ma)