Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, shagube dangane da jagorantar zanga-zanga zuwa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) don nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Wike wanda dan jam’iyyar PDP ne, amma ya nuna matukar farin cikinsa kan yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed, ya samu nasarar zama zabebben Shugaban kasa kan cewar Tunibun ya fito daga Kudu.
- Mataimakiyar Wike Ta Lashe Zaben Sanatan Ribas Ta Yamma
- Kotu Ta Umarci Jaridar ‘THISDAY’ Ta Biya Wike Miliyan 200 Kan Bata Masa Suna
Wike wanda ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar ranar Litinin lokacin da yake kaddamar da aikin hanyar da ta tashi daga Chokocho zuwa Igbodo a karamar hukumar Etche da ke jihar.
Gwamnan ya ce ai tun ba yau ba, ya gargadi shugabannin jam’iyyar dangane da nacewa da suka yi na cewa dole sai sun bar wa ‘yan arewa tikitin shugaban kasa da kuma shugaban jam’iyyar na kasa dukka a lokaci guda.
Ya ce, “Yayin da wasu suka shagaltu da yin zanga-zanga, ni kuma kaddamar da ayyuka ne a gaba na don na sanya jama’ata cikin farin ciki da annashuwa.”
Wike ya kuma jinjina wa ‘yan Nijeriya bisa zabin dan kudu da suka yi a matsayin shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a zaben da suka gudana.
Gwamnan ya kara da cewa, “Sashi 7(3)(c) na kundin tsarin mulkin PDP sun tanadar da tsarin karba-karba na shugaban kasa amma shugabannin jam’iyyar suka take wannan tsarin dokokin.