Gwamnatin Bauchi ta samu rarar kudi naira Biliyan Daya daga Kananan hukumomi 20 na jihar da ke shiga aljihun ma’aikatan bogi tsawon shekaru.
A halin yanzu, albashin kananan hukumomin Naira biliyan 2.9 ne bayan an rage shi daga Naira biliyan 3.2.
Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Mohammed Kashim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi a wani taro da kungiyar kwadago a Bauchi ta Shirya.
Ya ce lokacin da Gwamnatin Bala Abdulkadir Mohammed ta hau kan karagar milki a shekarar 2019, jihar Bauchi tana biyan Naira biliyan N3.5bn a matsayin albashin ma’aikata a kowanne wata.
Amma bayan nasarar gama tsame Ma’aikatan bogi, Kashim ya ce gwamnatin jihar Bauchi yanzun tana biyan Naira biliyan N2.8bn ga ma’aikatan jihar a karshen kowane wata.
Ya ce, Ma’aikatan jihar ba sa bin Gwamnatin albashin ko wata guda, inda ya ce sassan ma’aikata a jihar da ke korafin rashin samun albashinsu, ma’aikatan bogi ne kawai da aka gano acikin ma’aikatan jihar da kuma kananan hukumomi.