Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ja kunnen masu zuwa da karnuka ko wasu nau’ikan dabbobi rumfunan zabe musamman a ranar zabe.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar, ta ce sashe na 126 na dokar zabe ta 2022 ya bayyana karara cewa yin hakan saba doka ne, kuma laifi ne da aka tanadar wa hukunci karkashin dokar rike makami domin razana masu kada kuri’a da jami’an zabe.
- Gwamnan Kano Ya Yafe Wa Mutum 12 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa
- An Gabatar Da Shirin Sake Fasalin Cibiyoyin Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Don Tattaunawa
Sanarwar ta kara da cewa ana daukar karnuka a matsayin makamin da masu su ke amfani da su domin razanarwa ko cin zarafi ko raunata jama’a.
”Akidar zuwa da karnuka rumfunan kada kuri’a da masu zabe, ko wasu gungun mutane ke yi ba abu ne da za a lamunta ba, kuma muna kira da a dakatar da yin hakan, saboda ya saba da dokar zabe domin kuwa hakan na janyo razani da tsoratarwa”, in ji sanarwar.
Daga karshe sanarwar ta gargadi masu niyyar zuwa da karnuka ko sauran nau’ikan dabbobin rumfunan zabe da su guji yin hakan, saboda a cewar rundunar hakan saba dokar zabe.