Rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi, ta ce, ta sake shirin samar da isashshen tsaro domin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da tangarda ba a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar, CP Ahmed Magaji-Kontagora ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi a ranar Juma’a.
- Birtaniya Da Faransa Za Su Tattauna Kan Makomar Bakin Haure
- Ban Damu Da Hadakar PDP Da Sauran Jam’iyyu Ba -Uba Sani
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron wanda hukumar ta shirya domin hada kan masu ruwa da tsaki a harkar siyasa ya samu wakilai daga jam’iyyun siyasa daban-daban na jihar da kuma wakilan Sarakunan gargajiya na jihar.
CP ya ce, makasudin taron shi ne duba yadda al’ummar jihar suka gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da kuma tsara hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da zaben gwamna cikin lumana da nasara da kuma rashin cikas.
“Ba mun taru nan ne don yin fada ba amma mun taru ne don yin mu’amala da tunani kan yadda za a gudanar da zabe cikin lumana, ba tare da cikas ba, cikin nasara da kuma karbuwa a zaben gwamna mai zuwa,” in ji shi.
A yayin da yake yaba wa al’ummar jihar Kebbi bisa yadda suka fito domin gudanar da aikinsu cikin tsari a lokacin zaben da ya gabata, Magaji-Kontagora ya yi kira gare su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, su ba su goyon baya da ba jami’an tsaro hadin kai don ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya kuma bukaci iyaye da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su ja kunnen ‘ya’yansu maza da mata da masu goyon bayan jam’iyya kan aikata aikin ta ta’adanci, rashin da’a da duk wani abu da zai iya haifar da rashin zaman lafiya kafin zabe da kuma bayan zabe.
A karshe kwamishinan ‘yansandan Magaji-Kontagora ya yi kira ga ‘yan jarida da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ba tare da karkata a wani bangare ba, inda ya bukace su da su guji duk wani nau’i na labarun ban sha’awa don a samar da hanyar zaman lafiya a kasa.