• English
  • Business News
Tuesday, July 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwanturolan NIS Na Ribas Ya Ba Da Tabbacin Kare ‘Yan Kasashen Waje A Jihar

by Khalid Idris Doya
2 years ago
in Labarai
0
Kwanturolan NIS Na Ribas Ya Ba Da Tabbacin Kare ‘Yan Kasashen Waje A Jihar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) reshen Jihar Ribas, James Sunday, ya tabbatar wa ‘yan kasashen waje mazauna Nijeriya da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ke jihar, cewa su sha kuruminsu za a kare musu harkokin kasuwancinsu da hannun jarinsu gabanin da bayan zaben Nijeriya.

Da ya ke magana da ‘yan kasashen wajen ta kafar sadarwa, Kwanturolan ya jaddada kokarin da hukumar NIS ke yi wajen taimaka wa wadanda ba ‘yan Nijeriya ba, ‘yan kasashen waje da ke zaune a Nijeriya, ‘yan kasashen waje da ke nemin izinin aiki, neman izinin zama da yin kaura ta musamman (SIS).

  • NIS Ta Kama Wasu Mata 11 Da Aka Yi Fataucinsu Zuwa Kasar Libiya

Kazalika da wadanda ba ‘yan Nijeriya ba (Maza) da ke neman auren mace ‘yar Nijeriya bayan cika dukkanin ka’idojin da hakan ke bukata da kuma wadanda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu bisa doka da ka’ida tare da cikakken izini ko wasu da ke da wani aikin yi na musamman a cikin kasar nan.

Ya kara da cewa dukkanin wadannan rukunin mutanen (Yan kasan waje) da su kwantar da hankalinsu su ji kamar a gidajensu ko kasashensu na asali su ke domin cigaba da bunkasa harkokin kasuwanci.

Labarai Masu Nasaba

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

A cewar wata sanarwar daga sashin yada labarai na hukumar a jihar Ribas, James ya kuma bukaci ‘yan kasashen wajen da su cigaba da mutunta dokoki da ka’idojin Nijeriya da aka shimfida musu tare da bada wa ‘yan Nijeriya suke aiki da su domin rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

‘Yan kasashen waje mazauna Ribas sun samu tabbacin cewa za a basu cikakken kariya da harkokin kasuwancinsu muddin za su cigaba da mutunta dokoki da ka’idojin dukkanin hukumomin da suka shafi shige da fice da kuma zama halastaccen masu zuba hannun jari a Ribas da ma Nijeriya.

James Sunday ya kuma ba su tabbacin cewa kofar su a bude take wajen kyautatawa da inganta kyakkyawar alaka a tsakanin hukumar ta NIS da ‘yan kasashen waje domin bunkasa hada-hadar kasuwanci da zuba hannun jari.

  • https://leadership.ng/leadership-award-a-landmark-history-for-me-nis-cg-jere/

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Da Dumi-Dumi: CBN Ya Ba Wa Bankuna Umarnin Su Fitar Da Tsofaffin Kudade — Soludo

Next Post

Tsohon Mai Horas Da ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Na Falcons, Ismaila Mabo, Ya Rasu

Related

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
Da É—umi-É—uminsa

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

3 hours ago
Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
Da É—umi-É—uminsa

Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

4 hours ago
Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje
Da É—umi-É—uminsa

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

7 hours ago
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas, Ya Yi Jimamin Rasuwar Buhari, Ya Ce Mutuwa Ce Da Ta Girgiza Shi
Da É—umi-É—uminsa

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

9 hours ago
Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja
Manyan Labarai

Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

11 hours ago
SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai
Labarai

SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai

12 hours ago
Next Post
Tsohon Mai Horas Da ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Na Falcons, Ismaila Mabo, Ya Rasu

Tsohon Mai Horas Da 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Falcons, Ismaila Mabo, Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

July 28, 2025
Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

July 28, 2025
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

July 28, 2025
Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

July 28, 2025
An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

July 28, 2025
Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

July 28, 2025
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

July 28, 2025
Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

July 28, 2025
Gwamnatin Sakkwato Ta Ƙaddamar Da Sababbin Motoci 30, Don BunÆ™asa Sha’anin Sufuri A Jihar

Super Falcons Sun Iso Abuja ÆŠauke Da Kofin WAFCON

July 28, 2025
Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

July 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.