‘Yan kasuwar singa da ke Kano sun yi kira ga gwamnatin tarayya da na Jihar Kano da su kawo musu dauki domin rage musu radadin da suke ciki.
Da yake zantawa da LEADERSHIP a ranar Talata, daya daga cikin ‘yan kasuwar, Alhaji Abdulkadir Singa, ya ce kiran ya zama wajibi domin a shawo kan iftila’in da ya samu ‘yan kasuwar.
- Zaben Gwamnoni: INEC Ta Gargadi Jam’iyyun Siyasa Kan Tada Tarzoma
- Hatsarin Mota Sun Yi Ajalin Mutum 17, 17 Sun Jikkata A Bauchi
A cewarsa, akalla ‘yan kasuwa 500 a kasuwar ne gobarar ta shafa, wanda ta kone sama da shaguna 300.
Ya kuma kara da cewa rokon ya kuma zama wajibi duba da yadda akasarin ‘yan kasuwar da abin ya shafa na da mutane tsakanin biyar zuwa 10 da ke cin abinci a karkashinsu.
“Da yawa daga cikin ’yan kasuwar da suka yi asarar kayayyakinsu sakamakon gobarar na da mutane da dama da ke aiki a karkashinsu don nema wa iyalansu abin da za su ci.
“Don haka a madadin shugaban ‘yan kasuwar, ina kira ga gwamna Abdullahi Ganduje da shugaban kasa Muhammadu Buhari da su tallafa mana domin yawancin ‘yan kasuwar da abin ya shafa sun yi asara mai yawan gaske,” in ji shi.
Shi ma da yake jawabi, wani dan kasuwa, Shamsudeen Bello, ya ce abin takaici ne yadda gobarar ta auku a lokacin da jama’a suke shan wahala sakamakon manufofin gwamnatin tarayya na musayar kudi.
Ya ce gobarar da ta tashi tare da batun sabbin Naira ba wai kawai ta dagula matsalar ba, har ma da gurgunta harkokin kasuwanci a kasuwar.
Don haka ya bukaci Gwamnatin Jiha da ta Tarayya da su taimaka wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa domin rage musu radadin da suke ciki.
Sai dai ya yaba da kokarin jami’an hukumar kashe gobara ta jihar da wasu kamfanoni masu zaman kansu kan yadda suka shiga cikin lamarin a kan lokaci.