• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin Na Musamman Ya Karyata Zargin Dake Cewa Wai Kasarsa Na Saka Wa Afirka “Tarkon Bashi”

by CMG Hausa
3 years ago
Afirka

Wakilin musamman a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin mai kula da yankin kahon Afirka, Xue Bing, ya karyata kalamai marasa tushe dake cewa, wai kasar Sin tana saka wa Afirka “tarkon bashi”.

Xue, ya bayyana a shekaran jiya Talata a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, cewa bai dace a dora wa kasar Sin laifin sanya wa Afirka bashi ba.

  • Shanghai Ta Kara Shigar Da Ridi Daga Afirka

Alkaluman da bankin duniya ya fitar a bara sun nuna cewa, daga cikin bashin dala biliyan 696 da ake bin kasashen Afirka 49, kaso 75 bisa dari bashi ne na cibiyoyin hada-hadar kudi na bangarori daban-daban da ’yan kasuwan dake samar da bashi, abun da ya dauki akasarin bashin da ake bin kasashen Afirka. Kana akwai kaso 35 bisa dari na bashin da cibiyoyin samar da bashi masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya ke bin kasashen Afirka, adadin da ya ninka kusan sau uku idan aka kwatanta da bashin da kasashen Afirka suka karba daga kasar Sin.

Domin taimakawa kasashen Afirka rage matsin lambar da suke fuskanta a fannin biyan bashi, kasar Sin ta shiga cikin “shawarar dakatar da biyan bashi” da kasashen G20 suka fitar, da rattaba hannu tare da kasashen Afirka 19 kan yarjejeniyar dakatar da biyan bashi, ko kuma cimma matsaya daya kan ragewa ko soke bashi baki daya. Amma akasin haka, wadanda suka fi sauran bangarori bayar da bashi ga kasashen Afirka, ciki har da masu samar da bashi masu zaman kansu na kasa da kasa, da cibiyoyin hada-hadar kudi na bangarori daban-daban, har yanzu ba su dauki matakan ragewa ko kuma soke bashin da suke bin kasashen Afirka ba.

A dayan bangaren kuma, Xue Bing ya ce, kasar Sin na goyon-bayan kasashen yankin kahon Afirka don su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a wannan yanki.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Bugu da kari, a yayin taron manema labarai da aka shirya yau, wani dan jarida ya yi mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin tambayar cewa: Mene ne ra’ayin kasar Sin game da hadin gwiwa tsakanin kasashe da yankin kahon Afirka?

Wang Wenbin ya ba da amsa cewa, a halin yanzu, Habasha na kan wani muhimmin mataki na dawo da zaman lafiya, da mayar da hankali kan bunkasuwa. Mun yi imanin cewa, ya kamata dukkan kasashe su kara yin ayyukan da za su taimaka wajen ci gaban Habasha da samar da zaman lafiya a yankin baki daya, maimakon kakaba takunkumi don tilastawa ko tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe kan wasu batutuwa masu sarkakiya. Kasar Sin tana son yin aiki tare da ragowar kasashen duniya, don taimakawa yankin na Afirka ya zama ginshikin zaman lafiya da hadin gwiwa da samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa.

A dangane da batun kare hakkin bil Adama a kasar Amurka kuwa, Wang Wenbin ya ce, abin da ya dace gwamnatin Amurka ta yi shi ne, ta hanzarta magance matsalolin kare hakkin dan-Adam da ke kara ta’azzara a kasarta, kamar nuna wariyar launin fata, laifuffukan kyama, da matsalar harbin bindiga, da laifukan muggan kwayoyi da dai sauransu. (Mai fassarawa: Murtala Zhang, Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Wakilin Sin Ya Bayyana Rashin Gamsuwa Da Yadda Amurka Ta Gabatar Da Daftarin Kudurin Kwamitin Sulhu Kan Sudan Ta Kudu

Wakilin Sin Ya Bayyana Rashin Gamsuwa Da Yadda Amurka Ta Gabatar Da Daftarin Kudurin Kwamitin Sulhu Kan Sudan Ta Kudu

LABARAI MASU NASABA

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu

October 26, 2025
Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.