Wata kotu dake Ciudad de la Justicia da ke birnin Barcelona a kasar Spaniya ta yankewa tsohon dan wasan Barcelona da tawagar kasar Kamaru, Samuel Eto’o hukuncin watanni 22 na jeka gyara halinka bayan ya amsa laifin cogen harajin fam miliyan 3.2 a lokacin da yake buga wasa a Barcelona.
Har ila yau, alkalin kotun yace Eto’o zai biya kudin da ake binsa, da kuma tarar fam miliyan 1.55.
Chelsea Tana Tattaunawa da Manchester City Kan Sayalen Sterling
Tun da farko dai masu shigar da kara a kasar ta Sipaniya sun zargi tsohon dan wasan na Inter Milan da Chelsea, Eto’o da kin bayyana kudaden shiga da aka yi tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2009.
Tsohon dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo shima an taba gurfanar dashi a gaban kotu saboda yin cogen biyan haraji sannan Lionel Messi da Jose Mourinho da kuma Neymar suma an taba kaisu kotu da irin laifin.
Kawo yanzu dai Eto’o mai shekara 41 a duniya, wanda shi ne shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru a yanzu haka, ya koma Barcelona a shekarar 2004 yana da shekara 23 a lokacin sannan ya buga wasa a Real Madrid da Inter Milan da Chelsea da kuma Everton, wanda ya yi ritaya a 2019.
Banda Eto’o, kotun ta kuma samu tsohon wanda ya kula da harkokin kwallon dan wasan mai suna, Jose Maria Mesalles, wanda shima aka ci tara aka kuma yi masa daurin jeka gyara halinka na watanni 12.