Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, (INEC) ta bayyana Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Injiniya Yakubu Danladi-Salihu, a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Ilesha-Gwanara da aka gudanar ranar Asabar.
Danladi-Salihu wanda ya tsaya takarar a karkashin tutar jam’iyyar APC, ya doke babban abokin hamayyarsa, Usman Abubakar na jam’iyyar PDP.
- Ana Tsimayin Karbar Sakamakon Zaben Gwamna A Bauchi
- Ina Da Kwarin Guiwar Samun Nasarar Tazarce -Matawalle
Da yake bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben mazabar Ilesha/Gwanara, jami’in zaben, Dakta Adewale Rafiu, ya ce Danladi-Salihu ya samu kuri’u 14,949 yayin da babban abokin hamayyarsa, Usman Abubakar na PDP ya samu kuri’u 2,072.
“Yakubu Danladi-Salihu na APC bayan ya cika sharudan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar,” in ji Rafiu.
A jawabinsa na godiya, Danladi-Salihu ya gode wa al’ummar mazabar Ilesha-Gwanara bisa goyon bayan da suka ba shi har ya kai ga nasarar da ya samu a zaben majalisar dokokin jihar, inda ya tabbatar da cewa zai ci gaba da ba da fifikon jin dadinsu.
“Ina mika godiyata ga ‘yan mazabata bisa nuna kauna da goyon bayan da suka nuna min wajen sake zabata,” in ji shi.