Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa, za ta yi nazari kan zarge-zargen cin zarafin masu jefa kuri’a da sauya sakamakon zaben 2023.
INEC ta kuma koka akan sace wasu ma’aikatanta da cin zarafinsu da kuma kashe mata wani ma’aikacinta a lokacin gudanar da zabukan.
- Da Dumi-Dumi: Gwamna Bala Ya Doke Tsohon Hafsan Sojin Sama Ya Lashe Zaben Bauchi
- PDP Na Zargin Gwamnan Zamfara Da Yunkurin Murde Sakamakon Karamar Hukumar Maradun
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban ilimantar da kan masu jefa kuri’a Festus Okoye ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja.
Ya ce, tun farko INEC ta sanar da harin da ‘yan bangar siyasa suka yi wa ofis dinta da ke karamar hukumar Obingwa ta jihar Abia a lokacin tattara sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki.
Ya ce, hukumar za ta ci gaba kare mutuncin masu kada kuri’a, inda ya kara da cewa, hukumar ba za ta yi sako -sako wajen daukar mataki ba don binciko zargin almundanar da aka aikata na cin zarafin masu jefa kuri’a ba don yin nazari akai.
A cewarsa, wasu daga cikin ma’aikatan mu an sace su, wasu an ci zarafin su wasu an kwantar da su a asibiti an kuma hallaka daya.
Sai dai, Okoye ya koka kan yadda aka tayar da hargitsi a wasu wuraren da aka shirya gudanar da zabukan tare da kuma lalata kayan zabe.
Kwamishin ya nuna jin dadin akan yadda aka kara samun inganta ayyukan hukumar musamman wajen tura kayan aiki zuwa rumfunan zabe akan lokaci, inda hakan ya bayar da dama wajen bude rumfunan zabe akan lokaci kamar yadda aka tsara da kuma yadda aka sake inganta na’urar zabe ta BVAS da kuma sauke sakamakon zabe na mazabu daga manhajar IReV.