Yau ce ranar dazuka ta duniya karo na 11, kuma taken ranar ta bana shi ne “Dazuka da Lafiya”. Yankin dazukan kasar Sin ya ci gaba da bunkasa, haka ma ingancinsu, hakan ya sa ta zama kasa mafi saurin karuwar albarkatun gandun daji a duniya.
A halin yanzu, yankin gandun daji na kasar Sin ya kai kadada miliyan 231, wanda yankin dajin da aka shuka ya wuce kadada miliyan 87.6, wanda ya zama na farko a duniya.
Kasar Sin ta dauki kwararan matakai wajen kiyaye tsaunuka, koguna, dazuzzuka, da filaye, da tabkuna, da ciyawa, da kiyaye kwararowar hamada a cikin dogon lokaci da kuma bisa manyan tsare-tsare. Wannan ba wai kawai ya taimaka wajen kiyaye muhalli da kawata tsaunuka da koguna da kasa da garuruwa da kauyukan kasar Sin ba, har ma ya taimaka wajen kara yawan gandun daji na duniya. (Amina Xu)