Shugaba Muhammadu Buhari ya kare matakin da gwamnatinsa ta dauka na bijirewa shawarar Hukumar Bada Lamuni ta Duniya (IMF), wajen cire tallafin man fetur, ya ce halin da wasu kasashe suka tsinci kansu sakamakon cire tallafin man fetur, izina ce ga Nijeriya.
Yayin da yake amsa tambayoyi daga Jaridar Bloomberg, shugaban ya ce su kansu manyan kasashen duniya da suka cire tallafin yau suna yabawa aya zaki saboda illar da matakin da suka dauka ya haifar musu.
- Zanyi Iya Yina Domin Ganin Kwankwaso Ya Zama Shugaban Kasa- Bulama Bukarti
- Hajjin Bana: NCAA Ta Ziyarci Filin Jirgin Gombe, Ta Ce Filin Zai Yi Jigilar Alhazai
Buhari, yace gwamnatinsa a 2021 ta kaddamar da shirin cire tallafin, amma bayan tuntuba mai zurfi daga masu ruwa da tsaki, da kuma halin da ake ciki a 2022, daukar matakin cire tallafin ba zai haifarwa kasar da mai ido ba.
Shugaban Buhari yace abinda ke gaban su shi ne bunkasa hanyoyin samar da tataccen man fetur a cikin gida da kuma bai wa ‘yan kasuwa damar shiga harkar, domin dama wa da su wajen kafa manya da kananan matatun mai kamar wanda kamfanin Dangote da BUA da Waltersmith suka samar.
Rahotanni sun ce Nijeriya ta kashe akalla Naira tiriliyan hudu karkashin wannan gwamnati, wajen biyan tallafin man fetur domin ganin jama’ar kasar sun sayi man cikin sauki.
Yanzu haka karancin man da kuma tsadarsa sun taimaka wajen samun hauhawar farashin kayan masarufi a cikin kasar.