Kungiyar kwadagon Nijeriya (NLC), za ta fara gagarumin yajin aiki daga ranar laraba mai zuwa don nuna fusata da yanda gwamnati ta kasa wadatar da ma’aikata da takardun kudin da za su rika yin cefane.
Shugaban kungiyar Kwadago ta NCL, Komred Joe Ajero ne ya sanar da umurnin a taron kungiyar a Abuja.
- FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA
- Zan Yi Mulki Da Kowa, Zan Rike Amanar Al’ummar Jihar Kaduna – Uba Sani
Sakamakon taron ya nuna kungiyar ta gaji da bukatar da ta mikawa babban bankin Nijeriya CBN, da ya wadatar da kudin amma sai kara ta’azzara lamarin ya ke yi.
Sakataren tsare-tsare na kungiyar Komred Nasir Kabir ya ce ‘yan kungiyar za su mamaye ofisoshin babban bankin, kuma an umurci ma’aikata su zauna a gida.
In za a tuna hukuncin kotun koli na yin amfani da tsoffin kudi tare sa sabbi ne ya dan sauya lamura, inda gwamnatin bayan jan kafa ta mika wuya don gudun kar a ci gaba da sukar ta cewa ba ta bin umurnin kotu.
Wata matsalar ita ce ta dan karen tsada da karancin man fetur, inda farashin ke bambanta daga nan zuwa can.
Yanzu dai za a jira a ga zafin da yajin zai yi a daidai lokacin da musulmi suka shiga azumin watan Ramadan.