Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara, ya amince da shan kaye a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Gwamna mai ci ya sha kaye a hannun dan takarar gwamnan PDP, Dauda Lawal Dare.
- Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum
- NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya
Gwamnan a wani sakon faifan bidiyo da ya aikewa al’ummar jihar, ya ce dole ne shi da dukkan magoya bayansa su amince da ikon Allah domin al’amura suna faruwa ne kawai da yardarsa, sannan ya yi fatan alheri ga zababben gwamnan yayin da yake tafiyar da harkokin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa a lokacin da ta fara aiki, ta gana da dukkan manyan masu ruwa da tsaki a jihar kan yadda za su iya kawo zaman lafiya ta hanyar tattaunawar zaman lafiya.
Sai dai ya koka da cewa har zuwa yau babu wani abu da ya fi rashin tsaro da ya janyo asarar rayuka da lalata dukiya.
Gwamnan ya bayyana cewa baya ga tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindiga, ya yi aiki tukuru don ganin cewa gwamnatinsa ta shigo da bangarori daban-daban na siyasa wuri guda domin samar da zaman lafiya da hadin kai a jihar domin jama’a su rika gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Gwamnan ya ce, “Mun samu sulhu a siyasance kuma hakan ya share fagen yakin neman zabe cikin lumana da kuma harkokin siyasa lafiya a jihar.”
Matawalle ya kuma nemi gafarar duk wanda ya sani ko bai sani ba ya bata masa rai ko ya cutar da su, sannan ya kara da cewa shi mutum ne kamar kowa kuma aikin Allah Madaukakin Sarki ne kadai ba shi da kuskure.
Ya kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da tausaya wa wadanda suka yi hasarar dukiya da sunan biki, inda ya jaddada cewa su fahimci cewa ba su da wani wuri sai jihar Zamfara.
Ya kuma yi kira ga gwamnati mai jiran gado da ta zage damtse wajen dawo da zaman lafiya a jihar tare da nuna jin dadin gwamnatin bisa jajircewa da aiki tukuru da jajircewar al’ummar jiharsu.