Allah Ya yi wa tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Gombe, Nasiru Abubakar Nono rasuwa.
Nono ya mutu a ranar Alhamis sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Abuja zuwa Jos.
- Magoya Bayan PDP Sun Yi Zanga-Zanga Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kaduna
- Gawuna Ya Taya Al’ummar Muslmi Murnar Fara Azumin Watan Ramadan
Tsohon dan majalisar, wanda ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin Jihar Gombe daga 2015 zuwa 2018, ya fito ne daga karamar hukumar Yamaltu-Deba a jihar.
A halin yanzu, gwamnan Jihar Gombe, Yahaya Inuwa, ya jajanta wa iyalan marigayin, inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, har ma da jihar da kuma Nijeriya baki daya.
Inuwa, a cikin sakon ta’aziyyar da ya aike, ya ce marigayi tsohon dan majalisar, dan siyasa ne mai tawali’u kuma mai kasa-kasa da kai, wanda ya shahara wajen sadaukar da rayuwar al’ummar mazabarsa da ma al’ummar jihar baki daya.
Gwamnan ya bayyana tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Nono ya nuna hazaka, dattako da jajircewa a lokacin da yake jagorantar majalisar dokokin jihar kuma ya samu karramawa da biyayya daga abokan aikinsa a lokacin.
Gwamna Inuwa, a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da abokansa na siyasa da kuma al’ummar karamar hukumar Yamaltu-Deba bisa wannan babban rashi da aka yi.