Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya tabbatar da tura takardun kudade zuwa bankunan kasuwanci da ke fadin kasar nan don rage karancin kudin da ake fuskanta a kasar.
CBN ya kuma umarci daukacin bankunan da ke fadin kasar nan da su tabbatar da sun yi aiki a ranar Asabar da Lahadi.
- Masanin Najeriya da Uganda da Zambiya: Demokuradiyyar Dake Damawa Da Jama’A Wata Nasara Ce Da Jama’ar Kasar Sin Suka Samu
- An Yanke Wa Wasu Mutane 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Legas
Mukaddashin daraktan sashen samar da bayanan bankin, Dakta Isa Abdulmumin ne, ya sanar da hakan a yau Juma’a a Abuja, inda ya ce CBN ya tura kudade masu yawan gaske ga bankunan kasuwanci da ke fadin kasar nan.
Ya ce CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su zuba takardun kudade a injinan ATM su kuma biya kudi a kanta a cikin makon nan.
Ya ce, gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, kana zai jagoranci sa ido don ganin bankunan sun bi wannan umarnin.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) a ranar Alhamis ta umarci ‘ya’yanta da su mamaye ofishin CBN da ke daukacin fadin kasar nan saboda karancin kudi da ake ci gaba da fuskanta.