• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Mamayar Tattar 4

by Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Tarihin Mamayar Tattar 4
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ci gaba daga shafi na makon da ya gabata

Dalillan da Suka Karfafa Yakin Tattar

Tun da farko yana da kyau mu gano dalillan da suka karfafa bayyanar wadannan mahalukai masu kama da aljanu:

  1. Tattar sun tun faro kasar Musulunci a daidai lokacin da al’ummar Musulmi take cikin rauni a kowane bangare. Ga dai rarrabar kawuna wadda Allah ya hana mu. Ga talauci wanda ya faru a sanadiyyar yawan ambaliyar ruwa da aka yi shekaru ana yi wanda ya kawo wahalar abinci da tsadar rayuwa. Ga kuma ‘yan rigingimu da aka yi ta yi tsakanin Ahlus-Sunnah da tsirarun ‘yan Shi’ar da waziri ya daure masu gindi. Ga kuma karancin soja wadanda waziri ya kokkore su daga aiki yana nuna ma halifa cewa, akwai bukatar kula da tattalin arziki, don haka bai kamata a kashe kudaden gwamnati a kan soji ba.
  2. Halifan daular Abbasiyya na wancan lokaci mutumin kirki ne, mai son addini amma ba shi da ikon kome a hannunsa in ban da a birnin Bagadaza. Halifa kawai ya zama wani dodo wanda ba a ko iya ganin sa. An rufe shi cikin gida daga shi sai barori da

kuyangi. Bai san abin da duniya take ciki ba, kuma ita ma duniyar ba ta san abin da yake ciki ba.

  1. Kananan daulolin musulunci sun yarda da shugabancin Bagadaza kamar daular Ayubawa da ta Gaznawa da ta Khuwarizmawa da duk sauran kananan daulolin Musulunci in ban da daular ‘yan Shi’a ta Masar da ta Sufaye a Moroko. Su kam ba su

ma amince da halifa ba. Amma duka wadannan daulolin tare da amincewar su da gwamnatin Sunnah ta Bagadaza ba su zaune lafiya da ita. An yi ta yake- yake wadanda suka raunana kowane bangare.

Labarai Masu Nasaba

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

Akwai wata dirama da ta faru a shekarar 529H a lokacin da sarki Mahmud ya yi yunkurin juyin mulki a kan Halifa Mustarshid, ya kuma ci nasara har da kama Halifa a hannu. Daga bisani kuma sarki “Sabjar” ya shiga tsakani bayan wani bore da

talakawa suka yi, ya sasanta har aka mayar da halifa a kan kujerarsa. Shekara daya bayan haka sai kuma sarki Mas’udu ya bayyana nasa tawayen, ya shelanta ya cire halifa ya nada kanin babansa Al- Muktafi, haka din kuma aka yi.

Bayan shekaru 11 aka samu wani rikici tsakanin halifa Muktafi da mai gidansa abinda ya jawo halifan ya sa aka rufe dukkan masallatai har tsawon kwana 3 ba a sallah cikin su. Bayan wasu shekaru 10 kuma aka sake wani ya mutsi tsakanin halifa da sarki Muhammad dan sarki Mahmud abin da ya jawo aka yi wata 2 ana zaman dar-dar a Bagadaza.

A takaice dai koda Tattar suka zo ba wani sarki da yake da karfi ko yake da cikakken hadin kai da wani in ban da Khuwarizm Shah. Don haka da gamawa da shi sai fili ya koma wayam; ba mai iya jayayya da su.

  1. A daidai lokacin da Musulmi suke cikin wannan rauni, sarakuna suka shagala da wasanni da sabon Allah, su kuma rundunar Tattar runduna ce kammalalliya. Duk inda suka zo basu bukatar kowa ya ba su ko igiyar daure rakumi. Suna da da wakai da

ra kuma da shanu wadanda suke cin namansu, da wadanda suke hawa kuma ba su bukatar a sauya masu dusa ko a ajiye masu kasari ko wani abinci, tonon kasa suke suna cin kwari da ciyawa da duk abin da ya samu. Ga su da yawan adadi wanda

mahaliccinmu kadai ya san iyakarsa. Ba su da tsoro, ba su ja da baya, ba su da jin kai ko miskala-zarratin ga mutane.

  1. Akwai wasu kura kurai da gangancin da sarakunan Musulunci suka yi musamman ma dai Khuwarizm Shah lokacin da ya kashe wasu ‘yan kasuwa da suka zo daga kasar Sin ba bisa ga wani dalili ba kuma ya kwace masu dukiya. A lokacin da wannan labari ya je ga Jinkizkhan sai ya aika masa wasika yana barazanar zai dau fansa, sai kuma Khuwarizmshah ya kashe jakadan ya sa aka aske gemun ‘yan rakiyarsa ya ce musu su je su kai labari.

Daga nan kuma sarki Khuwarizmshah ya je don yakar Tattar ya tarar sun fita zuwa Turkiyya don yaki da wani sarki ana ce masa Kashlokhan. Khuwarizm ya shiga garinsu, ya auka ma matansu da ‘ya’yansu amma bai bar garin ba sai da suka cim ma sa suka gwabza yaki mai tsanani. A cikin kwanaki uku suka kashe masa jarumawa Musulmi 20,000.

Tare da haka su ma sun yi hasarar rayuka ba iyaka. Tarihi ya ruwaito cewa, saboda yawan jinin da ya zuba na jama’a har zamewa dawa kai ke yi a cikinsa. 6. Kiristoci wadanda suka kasa karya lagon Musulmi a yakin Kuros (Crusade) ‘yan shekaru kadan a baya su ma sun taka rawa wajen kwadaitar da Tattar a kan kama kasashen Musulmi. Suka rinka nuna masu irin arzikin da ke cikin kasashen da saukin cin galaba a kansu.

A lokacin da Tattar suka kama kasashen Sham sun bayyana goyon bayansu ga kiristoci har su kan sa Musulmi su duka ma Kuros don wulakanta su.

  1. Akwai kuma tasirin munafukan Musulmi, ina nufin ‘yan Shi’ah. Tun a zamanin sarki Nasir dan sarki Mustadi’u bi amrillah wanda ya fi duk sarakunan daular Abbasiyyah dadewa (ya yi sarauta shekaru 47 daga 575H-622H) shi’anci ya fara karfi a cikin daular Musulunci saboda kisisinar da ‘yan Shi’ah suka yi ma sarki na aiko masa da takarda a sirrance rubuce da duk abin da ya yi a cikin dare, shi kuma sai ya yi tsammanin gaskiya ne Imaman Shi’ah sun sai gaibi kuma su ne ke fada masu sirrinsa. Alhalin kuwa yan leken asiri gare su daga cikin barorinsa. Wannan sarki – saboda shi’ancinsa – ya yi ta nuna ma Tattar goyon baya da ba su asirran Musulmi.

A kodayaushe yana aika masu wasiku. Sai na biyu shi ne sarkin garin Musil wanda ake ma lakabi da Al-Malik Ar- Rahim. Wannan sarki shi ma ya dade yana sarauta (tsawon shekaru 50), kuma dan Shi’ah ne da ya raya wasu al’adu da bukukuwa na kiristoci, ya kuma kulla alaka mai karfi da Tattar har da aurar da dansa Salihu ga ‘yar sarkin Tattar na wancan lokaci Hulako, duk da yake auren bai yi karko ba kuma ya haifar da rashin jituwa a tsakanin su amma dai ya ba da goyon baya da gudunmawa ga Tattar har ma mayakansa sun taimaka wajen yakar Bagadaza. Na uku shi ne uwa uba ga wannan al’amari, ina nufin Waziri Mu’ayyiduddin Muhammad Ibnu Ahmad Ibnul Alkami wanda ya hau mukamin waziri a zamanin sarki Musta’asim tsawon shekaru 14. Kuma ya yi iya kokarinsa ya daukaka shi’anci amma Ahlus- Sunnah suka rinjaye shi, sai ya bi ta hanyar hila da makirci kamar yadda muka riga muka fada.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BukharaTarihi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shinge 4 Da Sabon Gwamnan Zamfara Ya Tsallake Kafin Ya Doke Matawalle

Next Post

Gidan Da Aka Farmaka A Bauchi Ba Na Shugaban INEC Ba Ne – Oyekanmi

Related

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

2 hours ago
Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP
Manyan Labarai

Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP

15 hours ago
NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru
Manyan Labarai

NAF Ta Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

1 day ago
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu
Ilimi

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

1 day ago
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano
Manyan Labarai

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

1 day ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m

2 days ago
Next Post
Gidan Da Aka Farmaka A Bauchi Ba Na Shugaban INEC Ba Ne – Oyekanmi

Gidan Da Aka Farmaka A Bauchi Ba Na Shugaban INEC Ba Ne - Oyekanmi

LABARAI MASU NASABA

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.