A ranar Talata 21 ga watan Maris 2023 ne al’ummar Nijeriya suka tashi da labarin wata girgiza fagen siyasar kasar nan, inda aka sanar da cewa, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Dakta Dauda Lawal Dare, ya lashe zaben da aka yi na gwamna a ranar 18 ga watan Maris 2023 a Jihar Zamfara, inda ya yi waje rod da gwamna mai ci na jam’iyyar APC, Daklta Bello Matawalle.
Jami’in kula da zaben da aka yi, Farfesa Kasimu Shehu, ya sanar da cewa, sakamakon zaben da aka yi ya nuna cewa, Dauda Dare ya samu kuri’a 377,726 inda ya kayar da Matawalle wanda ya tashi da kuri’a 311,976.
Tuni aka barke da murnar wannan nasarar da Lawal na PDP ya samu a sassan jihar Zamfara dama Nijeriya baki daya, nasarar da ake gani lallai ta samu ne ta hanyar jajircewa da aiki tukuru daga Dan takarar Dakta Lawal da bangaren jam’iyyar PDP gaba daya.
Tabbas wannan nasarar ta Dauda Lawal bata zo da sauki ba, ya ci karo da shingaye da dama. Dauda wanda tsohon ma’aikacin Banki ne ya fuskanci shari’u da dama har zuwa makonni kadan kafin a fuskanci zaben, shari’un neman tabbatar da shi a matsayin dan takarar gwamnan Zamfara, amma cikin ikon Allah ya samu nasara a dukkan shari’un da ya fuskanta.
Tun farko a watan Satumba na shekarar 20022, wata kotun tarayya da ke Gusau ta soke takararsa kan cewa, taron da aka yi inda aka zabe shi a mastayin dan takarar ba halastacciya ba ne, wani tsohon dan majalisar tarayya ne mai suna Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya nemi kotu ta soke zaben, a cewarsa an tafka magudi a zabukkan da aka yi. Maishari’a Aminu Bappa ya soke zaben a ranar 25 ga wata Mayu 2022 inda ya nemi a sake gudanar da wani zaben fidda gwani.
Duk da cewa, Lawal ya sake lashe zaben fidda gwani da aka yi amma kotun ta kuma dakatar da aiwatar da zaben sa da aka yi.
Haka kuma Maishari’a Bappa ya sake soke zaben ya kuma zartar da cewa, jam’iyyar PDP ba za ta iya gabatar da dan takarar a jihar Zamfara a zaben 2023 gaba daya ba.
Amma Lawal bai sadakar ba, inda shi da Adamu Maina-Waziri, shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben fidda gwamni Kanal Bala Mande (mai Ritaya) suka daukaka kara a babban kotun daukaka kara na Sakwatto inda suka nemi kotu da soke umarnin.
A watan Janairu na 2023 babbar kotun a karkashin Maishari’a Abubakar Talba, ta yi watsi da hukunci inda ta sake amincewa da Dakta Lawal a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da za a yi.
Karin shinge
Duk da wadannan nasarorin da Lawal ya samu, sai gashi an daukaka karar zuwa kotun koli. Inda a ranar 6 ga watan Maris 2023, ya sake samun nasarar a kotun koli inda ta zartar da cewa, Lawal ne halastaccen dan takarar jam’iyyar PDP kuma shi ne zai tsaya mata takara a zaben 2023.
Haka kuma Lawal ya fuskanci shari’a daga hukumar EFCC, inda shari’ar ta kai ga kotun koli amma cikin ikon Allah Lawal ya samu cikakken nasara inda kotun ta wanke shi daga dukkan zarge-zarge.
Daga ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 Dakta Lawal Dare zai karbi ragamar mulki Jihar Zamfara daga hannun Bello Matawale inda zai cigaba da aiwatar da alkawuran da ya yi wa la’umma, muna fatan al’umma za su bashi dukkan goyon bayan da yake bukata don kai Jihar Zamfa tudun-mun-tsira.