Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa, za a iya fuskantar dumamar yanayi fiye da yadda aka saba fuskanta a Jihohi kamar Zamfara da Sokoto da dai sauransu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NiMet, Muntari Yusuf Ibrahim ya fitar, hukumar ta bayyana cewa, binciken da hukumar reshen yankin ta fitar, ya nuna cewa ana tsammanin dumamar yanayi da zai kai sama da digiri 40 nan da sa’o’i 48 masu zuwa.
A cewar sanarwar, “Sassan Kebbi, Sokoto, Zamfara, Taraba da Adamawa ana sa ran za a iya fuskantar dumamar yanayi na sama da digiri 40. Yayin da akasarin yankunan Arewacin kasar ana sa ran za a iya fuskantar zafi tsakanin digiri 35 zuwa 40. wannan ya hada da sassan Oyo, Kwara, FCT, Nasarawa, da Benue.”
Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa garuruwa irinsu Bauchi, Gombe, Maiduguri, da Yola na iya fuskantar barazanar matsanancin zafi.
Don haka hukumar ta shawarci mutanen da ke wadannan wurare da su rika shan ruwa mai yawa a cikin wannan lokaci.