Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da tabbatar da an kashe dukiyar jama’a a inda ya dace (SERAP), ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta binciki wasu gwamnonin Jihohi da mataimakansu kan zargin bangar siyasa da siyan kuri’u a zaben 2023 da aka kammala.
SERAP, wacce ta yi wannan kiran a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 25 ga Maris, 2023 mai dauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, ta kuma bukaci INEC ta nada wani kwamitin shari’a mai zaman kansa da zai binciki zargin tashe-tashen hankula da sauran laifukan karya dokar zabe da ake yi wa wasu masu rike da mukaman siyasa.
Kungiyar mai zaman kanta, a cikin wasikar da ta aike wa shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ta kara yin barazanar gurfanar da hukumar zabe gaban kotu idan har ba ta binciki wadanda ake zargi da aikata laifuka da masu daukar nauyinsu da suka aikata miyagun laifuka a lokacin zaben ba, kuma dole a gurfanar da kowaye a gaban kuliya tare da hukunta shi.