Dino Melaye, tsohon Sanatan Kogi ta Yamma ya mayar da martani kan ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na shirin yin ritaya daga siyasa.
Melaye ya ce maganar cewa Atiku zai yi ritaya daga siyasa ya hada hannu da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu karya ce.
- Sin Na Fatan Za A Samar Da Shirin Boao Na Kyautata Aikin Sarrafa Duniya Da Kara Amfanawa Jama’ar Kasa Da Kasa
- Amurka Ta Sake Zargin Kasar Sin Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Domin Yunkurin Siyasa
Ya siffanta labarin a matsayin karya wanda ya fito daga bakin wadanda ke tsoron siyasar Atiku.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin yakin neman zaben Atiku da Okowa, ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba mai rike da tutar jam’iyyar PDP zai dawo kan sharafinsa.
“Muguwar karya da farfagandar da ake ta yadawa cewa Atiku na shirin yin ritaya daga siyasa don ya hada hannu da Tinubu, karya ce mai muni, kuma ya kamata a yi watsi da ita. Haske da duhu ba su da alaka. ‘Yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu, Atiku zai dawo nan ba da dadewa ba.”
Atiku ya zo na biyu a zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sai dai ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben da aka yi.
Tuni dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu.