A halin yanzu ya zama dole asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya su manna sanarwar gargadi ga marasa lafiya da iyalansu na cewa likitoci da ma’aikatan lafiya na da hakkin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoron barazana ko tsoron hare-hare a kan su ba a yayin da suke gudanar da ayyukansu na ceto rayukan al’umma. Tabarbarewar al’amarin kai hare-hare a kan likitoci da jami’an kiwon lafiya a kasar nan ya kai ga haka musamman ganin yadda ake kara fuskantar karancin likitoci kasar nan, inda wasu kasashen duniya ke yi wa likitocinmu tayin kudade masu kauri tare da yanayin aiki mai dadin gaske.
Sai kuma ga shi wadanda suka zabi zama a cikin gida don aikin su na ceto rayukan al’umma suna kuma fuskantar hare-hare daga marasa lafiya da iyalansu. A ‘yan watannin nan an samu karuwar hare-haren a kan likitoci daga marasa lafiya da iyalansu da basu gamsu da wani abu da likitocin suka gudanar ba yayin jinyar ‘yan’uwansu ko kuma suna zargin sakacin Likitocin ne ya yi sanadiyyar rasuwar ‘yanuwansu. Daga dukkan alamu hukumomin asibitocin da jami’an tsaro da hukumomin garuruwan da asibitocin suke basu da karfin da za su iya kawo karshen wannan lamarin da yake karuwa a kullum.
Rahoton hari na baya-bayan nan ya faru ne ana ‘yan kwanaki kadan a shiga sabuwar shekarar nan a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara inda wasu iyalan mara lafiya daya mutu suka farmaki daya daga cikin likitocin asibitin abin da ya sa hukumar asibitin ta kwace gawar danuwan mutanen. Dalilin da mutane suka bayar na kai wa Likitan harin shi ne wai sakacinsa ne ya kai ga rasuwar danuwan nasu.
Hukumar asibitin ta nemi a tabbatar da hukunta mutanen da suka aikata wannan laifin yayin da kuniyar Likitocin asibitin suka yi yajin aiki na kwana biyar, amma daga dukkan alamu hare-haren na cigaba da aukuwa babu wata alama ta yiwuwar dakatar da dabi’a marakyau.
A bayaninsa, shugaban kungiyar likitoci na Jihar Kwara, Dakta Ola Ahmed, ya ce, a halin yanzu ire-iren wadanan hare-hare yana faruwa a kusan duk mako a sassan jihar abin da kuma yake zama tashin hankali ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya. A wani rahoto irin wannan lamarin ya faru a watan Fabrairu na shekarar 2022 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Akure ta Jihar Ondo, dan’uwan wani mara lafiya ne ya yi wa wani Likita dukan kawo wuka.
A wani al’amarin kuma, Shugaban Kungiyar Likitoci reshen Jihar Bauchi, Dakta Adamu Sambo a taron manema labarai da aka yi a watan Yuli na shekarar 2022, ya bayyana yadda aka kai wa wani Likita hari, inda yake cewa, “A ranar 8 ga watan Yuli na shekarar 2022, Dakta Mohammed Sani, wanda babban jami’in asibitin ne a Babban Asibitin garin Misau, a yayin gudanar da aikinsa wani danuwan mara lafiya ya kai masa hari da gatari da nufin kashe shi, ba zamu amince da wannan haukar a aikin mu na ceto rayuwar al’umma ba.”
“Koma menene koken mutane, ya kamata su mika kukan ne ga hukumar da ta dace maimakon daukar doka a hannunsu. Wannan mutumin ya shigo ba tare da sanin halin da ake ciki ba ya kama wani likitan ma da baya cikin wadanda suka yi jinyar dan’uwan nasa ya shiga saransa da gatari har sau hudu.”
Haka kuma a watan Agusta na shekarar data gabata, iyalan wata mara lafiya sun kai ma wani likiitan mata hari inda suka ji masa mummunan ciwo a kansa, kungiyar likitoci ta yankin Abuja sun nuna damuwarsu a kan hare-hare a kan likitoci da dukkan ma’aikatan lafiya a yankin dama kasar gaba daya.”
Kungiyar ta bayyana damuwarta musamman a kan sabbin likitoci dama wadanda suka tsufa in aka lura da yadda aka cusa lamarin hare-haren a asibitocinmu a ‘yan shekarun nan.
Wadannan hare-haren kamar yadda suke faruwa a Nijeriya yana nuna irin halin takaicin da al’umma ke ciki ne a Nijeriya a kan haka yakamata a nemo kwararru a bangaren kula da mutane masu fushi don a wannan lokacin kusan duk wanda ka taba zaka ga yana cikin fushi ne.
Tabbas ana fuskantar halin talauci, ga kuma tashin hankalin da harkokin ‘yanta’adda masu garkuwa da mutane suka dorawa al’umma da kuma halin tashin hankali da jami’an tsaronmu ke jefa mutane a ciki, lamarin yana matukar shafar tunanin al’umma, daga ka taba mutum sai kawai ya fashe maka. Bayan tabbatar da ganin an hukunta masu kai wa likitoci hari ya kamata hukumomin asibitocinmu su samar da yanayin bayar da shawarwari da magungunan warkar da damuwa ba wai kawai ga marasa lafiya ba har ma da iyalansu da masu jinyar marasa lafiyar gaba daya, musamman ganin wasu ‘yan’uwan basu iya fuskantar labarin mutuwar ‘yanuwansu, su kuma kyautata mu’amalarsu da iyalan marasa lafiya.
A matsayinmu na gidan jarida muna sane da sakaci da rashin iya aiki na wasu likitoci da ma’aikatan lafiya wanda hakan yakan kai ga rasa rayuwar marasa lafiyar da suke jinya. Kamar kowanne lokaci ba a kai ga hukunta su, a kan haka muke kira ga mahukuntan asibitoci su samar da kafar da iyalan marasa lafiya za su iya kai koke a kan likitoci da ma’aikatan lafiya a cikin gaggawa a kuma tabbatar da an yi cikakken bincikre tare da hukunta wanda aka a samu da laifi, wannan zai matukar taimaka wa tare da kwantar da hankalin iyalan marasa lafiya, rashin wannan ne yake haifar da daukar doka a hannun su.