Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta buga wasanni har guda tara a cikin watan Afirilu da ya hada da na gasar Europa League da Premier da kuma kofin alubale na FA Cup.
A wasanni taran da ungiyar za ta fafata a cikin watan Afirilun za ta yi Premier League shida da Europa League biyu da FA Cup daya kuma cikin wasannin za ta buga karawa biyar a Old Trafford, sannnan ta yi hudu a waje.
Tun farko wasa 10 ya kamata United ta fafata a cikin watan na Afirilu, amma ya koma 9, bayan da aka soke wanda ya kamata ta yi da ranar 22 ga watan kuma hakan ya biyo bayan FA Cup za ta kece raini da Brighton a wasan daf da arshe a filin was ana Wembley ranar 22 ga watan Afirilu.
Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu Manchester United za ta ziyarci Newacastle United a karawar Premier a filin was ana St James Park sannan cikin sauran wasannin Premier League da za ta buga, za ta karbi bauncin Brentford da Everton a Old Trafford, za ta je gidan Nottingam Forest.
Daga nan ta je gidan Tottenham, sannan ta are wasa na arshe a cikin watan Afirilu da karbar bauncin Aston villa sai Sebilla da za taziyarci United a filin Old Trafford a wasan farko a matakin kusa dana kusa dana arshe a Europa League ranar 13 ga watan Afirilu, sannan ta je Sifaniya wasa na biyu ranar 20 ga watan.
Manchester United wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana ta dauki Carabao Cup tana ta uku a teburin Premier League za ta buga daf da arshe a FA Cup da Brighton haka kuma za ta fafata da Sevilla gida da waje a zagayen kwata finals a Europa League.