Wata budurwa ‘yar shekara 28 mai suna Jennifer Ndubuisi a mazabar Awgu ta Arewa a jihar Enugu ta doke dan majalisa mai ci, Eneh Jane Chinwendu inda ta samu tikitin jam’iyyar APC a zaben majalisar dokokin jihar a 2023.
Ndubuisi ta lashe zaben ne da kuri’u 14 yayin da babban abokin hamayyarta, Nwabisi Elozie James ya samu kuri’u 11.
Duk da cewa an kalubalanci nasarar Ndubuisi, hakan yasa aka sake karawa amma duk da haka, Ndubuisi ta samu nasara da kuri’u 16, inda abokin hamayyarta ya samu kuri’u 9.
Ndubuisi ta godewa Mrs Ginika Tor, kwamishiniya a hukumar kula da dabi’u ta tarayya, saboda daukar nauyin zabenta da tayi ita daya tilo.
Ndubuisi wacce ta yi magana ta bakin mai magana da yawunta, Onyebuchi Dede, ta ce kungiyar Omaluegwuoku Progressive Initiative, wacce Misis Tor ta kafa tayi azumin nafila na kwana Uku don neman Ubangiji ya bata Nasara a Zaben fidda gwanin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp