Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nada tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Muhammad Attahiru Jega a matsayin uba ga sabuwar Jami’ar nazarin koyar da aikin malinta ta Kano, Kumbotso.
Kazalika Gwamnatin ta Kano, ta amince da nada Oba Dokta Moshood Olalekan Ishola Balogun Aliiwo a matsayin shugaban majalisar kula da ayyukan Jami’ar.
Gabanin zama shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shugabanci Jami’ar Bayero Kano tsawon shekaru biyar, haka kuma kafin haka, ya kwashe shekaru da dama yana koyar da ilimin kimiyyar siyasa a Jami’ar ta Bayero.
Kwamishinan labaran gwamnatin Kano, Malam Mohammed Garba wanda ya sanar da haka bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a ranar Lahadi, ya ce a kwanan nan ne hukumar kula da Jami’o’i ta Nijeriya wato NUC ta amince da daga likafar kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa matsayin Jami’ar nazarin koyon aikin malinta.
Kwamishinan ya ce sauran mambobin majalisar kula da ayyukan sabuwar Jami’ar sun hada da Dokta Muhammad Adamu Kwankwaso da Hajiya Zulaiha U.M Ahmed da Dokta Ibrahim Yakubu Wunti Dokta Halima Muhammad da kuma Alhaji Sabiu Bako.
A cewar Kwamishinan, Mlmajalisar zartarwar ta Kano ta amince da nada shugabannin da zasu tafiyar da ayyukan Jami’ar na yau da kullum, wadanda suka hada da Farfesa Isa Yahaya Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar da Kabiru Ahmed Gwarzo mataimakin shugaba mai kula da al’amuran karatu da Doktw Miswaru Bello mataimakin shugaba mai kula da harkokin mulki sai kuma Saminu Bello babban magatakarda na Jami’ar.
Sauran su ne Hajiya Mabruka Abubakar Abba shugabar sashin kula da dakunan karatu na Jami’ar yayin da aka nada Ibrahim Muhammad Yahaya babban jami’in kula da al’amuran kudade.
Ita dai sabuwar Jami’ar nazari da koyon aikin malinta ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, ita ce ta 61 a jerin Jami’o’i mallakar jihohi yayin da ta kasance ta 222 a jerin Jami’o’in Nijeriya.