A daidai lokacin da miliyoyin Yan Nijeriya suke daukin jiran rantsar da sabuwar gwamnatin sabon shugaban kasa da yan majalisun tarayya, wadanda aka zaba ranar 25 ga watan Fabarairun 2023; kwatsam sai wani rahoton jami’an tsaron DSS wanda ya nuna cewa sun bankado kumbiya-kumbiyar wasu bara-gurbin yan siyasa, maras kishin kasa, wajen kulla munakisar kifar da tsarin dimukuradiyya tare da maye gurbinsa da gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya.
Wannan labarin ya yi shigar shantun kadangare a zukatan ‘yan Nijeriya, a matsayin tatsuniyar da bata wuce ta gizo da koki ba, duk da cewa idan babu rami, to me ya kawo zancensa. Sannan babu kira me ya kawo karewar gawayi a makera? Saboda babu wani rikici ko hayaniyar da ta jawo an kasa gudanar da babban zabe ba, ko wasu matsalolin da suka jefa kasa cikin rashin tabbas, wanda zai jawo kiraye-kirayen kafa gwamnatin rikon kwarya da makamantan su.
Al’amari ne mai daure kai ace da rana tsaka, ana zaune kalau wasu tsiraru su bushi iska wajen yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya. Shin da yawun wa suke magana, kuma wa ya goya musu bayan da suka samu karfin halin kalubalantar zaben da yan Nijeriya suka yi? Duk da na san ruwa baya tsami a banza, amma ko shakka babu hakar wadannan yan siyasa ba zata cimma ruwa ba, saboda alamu sun nuna ba yan kasa suke wakilta ba, face wahamin shaidan.
Tun bayan bazuwar wannan rahoton, miliyoyin Yan Nijeriya sai tambayoyi suke yi; me ya jawo batun kafa gwamnatin rikon kwarya, bayan an riga an kammala zabe? Ko kuma zaben da yan kasa suka yi bai gamsar ba? Shin da zabe da kafa gwamnatin rikon kwarya wane ne yake da halasci a kundin tsarin mulki? Idan ba haka ba, a tsarin dimukuradiyya, shin Nijeriya tana tafiya kan ra’ayin wasu tsiraru ne ko na mafiya yawan yan kasa? Amma idan ba haka ba, kenan kuna nufin dama can wani abu ake yi daban da zabin yan kasa? Ya dace masu wannan yunkurin su amsawa wadannan tambayoyi na miliyoyin Yan Nijeriya.
Saboda ko a zaben da ya gabata yan Nijeriya sun nuna wa irin wadannan yan siyasa ba kanwar lasa bane, wanda hakan ya tabbatar da cewa yan kasa sun shirya kalubalantar rashin adalcin da gurbatattun yan siyasa, maras kishin kasa wadanda ba kasa bace a gaban su, face kawai bukatar kashin kansu. Wanda hakan ya tabbatar cewa wannan yunkurin ba zai kai gaci ba.
Babu wani dalilin da zai kawo batun kafa gwamnatin wucin gadi, sannan kuma koda akwai, yan Nijeriya sun dawo daga rakiyar yan siyasar kasar nan, musamman irin yadda abubuwa suke tafiya, wanda babu lafiyayyen dan Nijeriya da zai yarda da wannan hauragiya da sunan kafa gwamnatin wucin gadi.
Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Tsaron Kasar ta fitar, mai dauke da sa-hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Mista Peter Afunanya ya ce ta gano wasu manyan yan siyasar da ba ta bayyana sunayensu ba da hannu dumu-dumu wajen shirin kafa gwamnatin wucin gadin a kasar.
Hukumar DSS ta ce shirin zagon kasa ne wanda zai gurgunta mulkin dimukuradiyya tare da jefa kasar cikin wani mawuyacin hali maras dadi.
“Hukumar DSS ta gano wasu manyan yan wajen shirin kafa gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya. Ma’aikatar ta dauki wannan makirci, wanda wadannan bukatu masu karfi ke bi, ba wai kawai rugujewa ba ne amma wata hanya maras kyau ta jingine kundin tsarin mulki a gefe da kuma mayar da hannun agogo baya a tsarin dimokuradiyya tare da jefa kasar cikin rikici maras tabbas.”
“Ba za a amince da wannan matakin ba kwata-kwata a lokacin da tsarin dimokuradiyya ke gudsna a Nijeriya ga yan kasa masu son zaman lafiya. Kuma wannan makarkashiyar tana faruwa ne bayan gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a mafi yawan sassan kasar.”
Mista Afunanya ya ce wadannan yan siyasa sun yi taruka da dama inda ya ce suna shirin daukar nauyin zanga-zangar da za a yi a manyan biranen kasar wanda zai kai ga ayyana dokar ta-baci, wanda hakan zai kai ga dakatar da rantsar da sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu, mai zuwa.
Biyo bayan ikirari na yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi a Nijeriya, Hukumar DSS ta fuskanci matsin lamba kan ta bayyana sunayen wadanda ke da hannu a wannan aika-aikar.
Kiran da wasu fitattun yan Nijeriya da aka fallasa a siyasance suka yi ya ta’allaka ne kan imanin cewa bai kamata hukumar ta tsaya kawai wajen fitar da wannan rahoton ga jama’a ba, ya dace su dauki matakin kawar da “makiyan Nijeriya.”
Haka kuma, Hukumar DSS ranar Asabar sun ja kunen yan siyasa su guji kalaman batanci da yada labaran karya, al’amarin da zai jawo kyama ga gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da zababben shugaban kasa mai zuwa, Bola Tinubu.
Yan-sandan cikin, sun yi wannan kashedin ne biyo bayan korafin da karamin Ministan kwadago ya yi, Festus Keyamo tare da bukatar Hukumar DSS su gayyato dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi; da mataimakin sa, Dr. Datti Baba-Ahmed, sakamakon kin amincewa da suka yi da zaben Bola Tinubu.
Har wala yau, shima dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar wanda a watan Maris ya jagoranci zanga-zangar limana a ofishin hukumar INEC dake Abuja, inda ya bukaci soke zaben 25 ga watan Fabrairu da ya gabata.
Masu wannan yunkurin sun manta cewa gwamnatin wucin gadi da karshe kwanakinta 82 kacal ta gushe?
Idan ba a manta ba, gwamnatin rikon kwarya ta karshe a Nijeriya, kimanin shekaru 30 da suka gabata bata wuce tsawon kwanaki 82 ta kare ba.
An kafa gwamnatin rikon kwarya ne bayan zaben shugaban kasa na 1993, a lokacin marigayi Moshod Abiola, bayan da ya ayyana samun nasarar zaben ranar 12 ga watan Yuni, a zamanin mulkin soja a karkashin Janar Ibrahim Babangida. Gwamnatin wucin gadi, wadda Ernest Shonekan ya jagoranta.
A nasu bangaren, yan majalisar wakilan Nijeriya, sun bayyana matukar takaicin dalilin da suka hana hukumar DSS ta gayyato tsohon shugaban kasa Olusigon Obasanjo, tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar LP, Dr. Datti Ahmad, da makamantan su domin su amsa tambayoyi dangane da zarge-zargen hannun na kafa gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya.
A wani zaman da zauren majalisar wakilai ya gudanar tare da tabka zazzafan muhawara kan gaggauta kamo masu daukar nauyin kitsa yunkurin, kudurin da Hon. Unyime Idem, inda tayi kakkausan suka kan yunkurin. Majalisar ta kara da bayyana cewa kafa gwamnatin wucin gadi abu ne wanda ya saba wa kundin tsarin mulki kuma hawan kawara ne ga tsarin dimokuradiyya. Saboda haka zauren ya ankarar da jami’an tsaro su tashi tsaye wajen kare doka da oda.
Lokaci ya yi wanda yan Nijeriya za su yiwa kansu karatun ta-nutsu wajen fahimtar yadda abubuwa suke gudana a kasar nan, saboda yadda mafiya yawan wadannan yan siyasa maras kishin kasa.