Fitacciyar marubuciyar Hausa Hajiya Humaira Azare, ta bayyana tsantsar ra’ayi da sha’awarta ne a kan rubuta littafi fiye da rubutun fim, cikin wata tattaunawa da ta yi da wakilinmu Adamu Yusuf Indabo. Ga dai cikakkiyar yadda hirar tasu ta kasance.
Mene cikakken sunanki, da kuma takaitaccen tarihinki?
Sunana Humaira Kuda Azare, haifaffiyar cikin Azare karamar hukumar Katagum da ke cikin Jihar Bauchi. Na yi ‘primary da secondary’ har zuwa makarantar gaba da sakandire (higher institution) inda na karanci Islamic Education. Kuma ni matar aure, na yi aure tun shekarar da na gama secondary 2001. Allah ya albarkace ni da diya, Alhamdulillah. Diyata daya tana nursing Aisha muna mata lakabi da Ummi.
To Hajiya Humaira, sunanki fitaccen suna ne a duniyar rubutu. Ya aka yi kika tsinci kanki a matsayin marubuciya?
Na kasance ma’abuciyar karance-karance wannan ya sanya ni sha’awar fara rubutu, na yi nazari sosai a kan yadda zan tsara nawa rubutun wajen fadakar da ‘yan uwana a kan kishi, da karbar duk kaddarar da ta samu diya mace a gidan aure, ta karbe ta hannu bibbiyu, ta san cewa aure ibada ne ba son zucciya ko al’ada ba. Wannan ya sa littafina na farko na mishi lakabi da ZA KI IYA? Saboda sai cikakkiyar jaruma mai tauhidi za ta iya karbar diyar da ta rike tun ba ta wuce shekara biyu ba, a wayi gari ta zamo abokiyar zamanta.
Wacce shekara kika fara rubutu?
Na fara rubutu a shekara ta 2011, inda na fara da ZA KI IYA? Bayansa na rubuta AYYANA sai kuma BA ZAI WARWARU BA. Su ne littattafaina guda uku wadanda na rubuta kuma aka wallafa. Daga nan harkar rubutu ya tsaya min cak, sakamakon yanayin kasuwa na sa kudadena ba su fita ba balle a kai ga riba. Sai dai an samu abinda ya fi riba wato jama’a Alhamdulillah. Amma dai yanzu haka na rubuta wasu littattafan su ma guda Uku wadanda ba a kai ga bugawa ba su ne: YAU DA GOBE, da KUKAN KURCIYA da kuma KOWA YA SAYI RARIYA. Na ajiye su saboda yanayin yadda kasuwar take.
Ke nan tun wancan lokacin dama akwai matsalar kasuwa, ba wai yanzu ne da marubutan online suka yi bozo ya murkushe kasuwa ba?
Eh tun wancen lokacin akwai matsalar kasuwa, sai dai ba irin ta yanzu ce da littafin ba ya sayuwa ba. Za a siyar da littafi amma kudin ba su dawowa, sai a sake fidda wasu ake buga wani. Zuwan online ya sa makaranta ba su damu da littafin kasuwa ba, sun ma fi karanta na online musamman wanda za ana turo musu shi a kyauta kullum suna karantawa har a gama.
To cikin littafanki da aka samu bugawa. Wanne ne ya fi karbuwa ga makaranta?
ZA KI IYA? Shi ya fi karbuwa saboda an kira ni a waya ba adadi, gaskiya kuma na samu jama’a sosai wadanda muke zumunci sosai a garuruwa da dama. sai kuma ba zai warwaruba har akwai wadda ta kira ni akan ita ma hakan ya faru da ita, sun dau haramtaccen jini sun mai da shi halal, shi ne an dau jinsin kanin mijinta an hada da nata saboda mijinta bai ya haihuwa. Wannan nasaba haramtaccen samar da jini ne, abu ne da ba zai warwaru ba sai a lahira. Yana da kyau kafin mutum ya aikata abu ya nemi sani a wajen maluma. Na samu mutane sosai shi ma.
Cikin littattafanki guda 6, wanne kika fi shan wuya wajen rubuta shi?
Gaskiya na sha wahala wajen rubuta ba zai warwaruba, saboda sai da na research sosai wajen malamai da kuma likitoci. Ya kunshi hada kwai (IBF) ga wanda suke da matsalar rashin haihuwa, in na ma’auratan ne ya halatta. Amma su wannan na kanin mijin ne aka hada wanda bai halatta ba a addinin musulunci. Wallahu a’alam.
Juyin zamani ya sa marubuta tsallakawa rubutun fim. Ke mene naki ra’ayin game da haka?
Eh to ni dai ra’ayina da karashina yana ga rubutun littafi, ba ni da sha’awa akan firm gaskiya.
Daga fara rubutunki zuwa yau, wadanna nasarori kika cimma ta dalilin rubutu?
Nasarorin da na cimma dai mu’amala da mutane, ta yanda na zamo mai gyara lamuran aure da ba da shawarwari ga jama’a. Wannan babbar nasara ce ya zamo kana samun gudanar da aikata alkhair.
Wanne kalubale kika fuskanta daga fara rubutunki zuwa yau?
Gaskiya ban samu kaina a wani kalubale ba, in ka dauke maganar yadda kudade suka makale a kasuwa, wanda tuni na yafe Allah ya yafe mu baki daya.
Wacce shawara za ki ba wa makaranta da kuma ‘yan uwanki marubuta?
Shawara da zan bawa marubuta shi ne su yi kokarin kula da alkalaminsu wajen rubuta abinda zai amfanar da al’umma, kada su tsunduma kansu cikin hatsarin rubuta shirme, wanda za ai kuka da su wajen gurbata tarbiyya.
Wanne sako kike da shi ga masoyanki?
Sakon da zan isar ga masoyana shi ne Allah ya sa mu mu wanye da duniya lafiya ina godiya.
To Hajiya Humaira mun gode.
Ni ce da godiya.