A yau ne, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labarai, inda kwararrun da abin ya shafa suka gabatar da matsayin bincike game da gano asalin kwayar cutar COVID-19 a kasar Sin.
Darektan hukumar yaki da cututtuka ta kasar Sin, Shen Hongbing ya bayyana cewa, sama da shekaru uku ke nan da aka gano cutar COVID-19 a karshen shekarar 2019. A cikin wannan lokaci, kasar Sin tana ci gaba da inganta aikin binciken gano asalin kwayar cutar. Gwamnatin kasar Sin da masanan kimiyyar kasar sun ci gaba da martaba matakai na kimiyya, suna kuma tattaunawa da yin hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya.
Mai bincike a cibiyar yaki da cututtuka ta kasar Sin Zhou Lei ta bayyana cewa, a yayin da ake gudanar da binciken hadin gwiwa da kwararru na kasashen waje, masana kimiyyar kasar Sin sun ba da dukkan bayanan da suke da su bisa ka’idojin kimiyya, ba tare da wata rufa-rufa ba, bisa sanin ya kamata da gaskiya.
Shugaban kwalejin harkokin rayuwa a jami’ar fasahar binciken sinadarai ta Beijing, farfesa Tong Yigang ya bayyana cewa, a halin yanzu babu wani tushe na kimiyya da zai fayyace ainihin asalin COVID-19. (Mai fassarawa: Ibrahim)