Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 18 zuwa 21 ga watan Afrilu.
A yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru cewa, ya yi imanin cewa, ziyarar shugaba Bongo za ta kara sa kaimi ga bunkasuwar alakar dake tsakanin kasar Sin da Gabon, da inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen biyu, da ci gaba da samun sabbin sakamako.
Ban da haka, Wang ya ce, a kwanan baya ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya halarci taron ministocin harkokin waje na kasashen dake makwabtaka da Afghanistan karo na hudu a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan. Taron ya kuma fitar da sanarwar Samarkand na taron ministocin harkokin wajen kasashen da ke makwabtaka da kasar Afghanistan karo na hudu. (Ibrahim)